Obasanjo ya yi rijista da sabuwar kungiyarsa

Obasanjo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Obasanjo ya shawarci Shugaba Buhari da kada ya yi tazarce a 2019

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi rijista da sabuwar kungiyarsa mai rajin ceto Najeriya daga halin da take ciki, mai suna Coalition for Nigeria Movement (CMN), a ranar Alhamis.

Ya yi wa sabuwar kungiyar ne rijista a sakatariyar 'yan Jarida da ke garin Abeokuta na jihar Ogun wato a mahaifarsa a kudancin Najeriya, kamar yadda wani na kusa da tsohon shugaban ya shaida wa BBC.

A bayaninsa yayin rijistar, Obasanjo ya ce duka manyan jam'iyyun kasar biyu wato APC da PDP ba za su samu nasara ba a babban zaben kasar wanda za a yi a shekarar 2019.

"Wannan kungiyar wata tafiya ce ta jama'a kuma za ta samu nasara a shekarar 2019," in ji shi.

An fara kaddamar da kungiyar ne a cibiyar Yar'adua da ke Abuja ranar Laraba kuma akwai tsofaffin 'yan siyasar kasar da suka samu halartar taron.

Tsohon gwamnan jihar Osun Olagunsoye Oyinlola ne jagoran kungiyar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya bayyana.

Sai dai tsohon shugaban ya ce zai janye jikinsa daga kungiyar da zarar ta zama jam'iyyar siyasa.

A makon jiya Cif Obasanjo ya rubuta wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wata doguwar wasika, wadda a ciki yake ba shi shawara da kada ya nemi tazarce a shekarar 2019.

A nan ne kuma ya bukaci kafa wannan sabuwar kungiyar don ta cire wa 'yan kasar kitse a wuta.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Wasikun Obasanjo ga Shugabannnin Najeriya

Labarai masu alaka