APC ta ya da tsintsiya ta dauki makami —PDP

PDP ta zargi APC a jihar Kano da bangar siyasa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption PDP ta zargi APC a jihar Kano da bangar siyasa

Babbar jam'iyyar adawa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, wato PDP, ta zargi jam'iyyar APC mai mulki a jihar da jefar da tsintsiya da kuma daukar makami.

PDP dai ta ce, APC da magoya bayanta, na kokarin bata siyasar Kano ta hanyar rungumar bangar siyasa a tarukanta, musamman ma a wannan lokaci da ake tunkarar zaben kananan hukumomi, lamarin da ta ce, babban ci baya ne ga demokradiyya.

PDP ta ce, kamar yadda ta ke zargi, yanzu APC, babba da yaro kowa ya koma yawo da makami inda ta jaddada cewa, bai kamata mai dokar bacci ya buge da gyangyadi ba.

Alhaji Musa Danbirni, shi ne kakakin jam'iyyar ta PDP a jihar Kano, ya kuma shaida wa BBC cewa, "Yanzu APC, ta ajiye tsintsiya ta dauki makami, don haka yanzu a jihar Kanon, an shiga halin ha'ula'i saboda tsoron abin da zai iya faruwa a zaben 2019, saboda tun ba a je ko ina ba, mutane na yawo da makamai".

To sai dai kuma jam'iyyar APC anata bangaren, ta ce adawa ce ke hana PDP fadar alkhairi a kanta, kuma a iya saninta, ko cacar baki magoya bayanta ba sa yi da 'ya'yan kishiyoyinta ma, ballanta su yi fada su ya su a cikin gida.

Honourable Mustapha Hamza Buhari ba kwana, shi ne mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara a kan harkokin siyasa, ya kuma shaida wa BBC cewa, "Doka ce ta gwamnan jihar Kanon cewa, idan zaka bishi bai yarda ka rike makami ko gora ko makamancin haka ba."

"Don haka wannan maganganu ne na abokan adawa, kuma a Kano, ba a siyasar banga, ba a kuma siyasar cin mutunci".

Fargabar bangar siyasa a Kano dai, ta karu ne a dan tsakanin nan, bayan wata 'yar tayar da kurar da bangaren tsagin Kwankwasiyya na jam'iyyar APC ya yi, da kuma wata ziyara da jagoransa sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya yi niyyar kai wa Kanon, a dai-dai lokacin da bangaren Gandujiyya ke zafafa tarukansa na siyasa.

Amma a yanzu za a iya cewa kurar ta dan lafa.

Labarai masu alaka