'Kifi sam ba zai iya maye gurbin nama ba'

Masu sayar da nama a Najeriya, sun ce nama na gaba da kifi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu sayar da nama a Najeriya, sun ce nama na gaba da kifi

Masu sayar da nama a Najeriya, sun ce suna da ja game da batun da masu sayar da kifi suka yi a jihar Kaduna da ke arewacin kasar, inda suka ce kifi zai iya maye gurbin nama.

Masu sayar da naman, sun ce ba bu yadda za ayi kifi ya maye gurbin nama, domin duk da kashe-kashen fulani da ake yi a arewacin Najeriya, ana samun shanu da yawa wadan da za a yanka a samu naman da za a ci.

Kazalika masu sayar da naman sun ce ba wai fulani ni kadai ke kiwon shanu ba, akwai mutanen da suke kiwonsu.

Wakilin BBC a jihar Kaduna, ya tattauna da wasu masu ta'ammali da nama, inda Umar Rilwan ya ce, " A gaskiya kifi ba zai iya maye gurbin nama ba, saboda akwai kwata-kwata wadan da ba sa ma cin kifin".

Shi kuwa Yusuf Adam, cewa ya yi " Hakika abin da ake tunanin zai iya yi wu wa, ba lallai ne ya yiwu a wajen wasu ba, saboda wasu a rayuwarsu ba sa son ma karnin kifi ballantana har suka kai ga ci, to amma nama da wuya ka samu wanda ba ya ci, sai dai a samu bambamci na dabbar da mutum yafi so".

To kamar dai yadda bahaushe ke cewa ba a rasa nono a ruga, wasu na ganin cewa duk da shekaru da aka kwashe ana rigingimu tsakanin makiyaya da fulani, rigingimun da wani lokaci kan jayo kiwo ya yiwa fulani wuya, ba a taba rasa saniya a ruga ba.

Labarai masu alaka