Gidajen yarin Nigeria 'kan mayar da mutane dabbobi'

Osinbajo Hakkin mallakar hoto EPA

Mataimakin shugaban Najeriya ya soki hukumar gidajen yarin kasar - yana mai cewa yanayin da daya daga cikin gidajen yarin ke ciki ya yi irin munin da zai sa wadanda suka shiga su fito tamkar dabbobi.

Yemi Osinbajo ya bayyana takaicinsa bayan ya ziyarci gidan yarin da ke birnin Fatakwal na jihar Rivers da ke kudancin kasar, wanda aka gina domin mutum 800, amma a halin yanzu yana dauke da sama da mutum 5,000.

An yi kiyasin cewa mutum 3,700 daga cikin wadanda suke gidan yarin suna jiran a yi musu shari'ah ne - yayin da wasu suka shaida wa mataimakin shugaban cewa sun shafe shekara biyar suna jira a kai shari'arsu kotu, kamar yadda jaridar Vanguard ta Najeriya ta ruwaito.

Mista Osinbajo, wanda ya ziyarci gidan yarin ranar Laraba, ya yi magana a lokacin da aka gabatar da wani rahoto game da halin da gidajen yari suke ciki a fadin kasar.

Ya ce: "Abin da na gani na da tayar da hankali domin gidan yarin ba shi da dakuna, sai dai yana nan ne a matsayin gidan ajiye kaya inda aka ajiye sama da da mutum 5000 maimakon mutum 800 da ake son su zauna a ciki.

"Daga abin da na gano, sun ce babu daki ga 'yan gidan yari kuma dukkan mutumin da ya shiga gidan zai dawo ne a matsayin dabba."

Mista Osinbajo ya nuna cewa yin gyara kan yadda ake tafiyar da gidajen yarin zai dauki lokaci mai yawa, amma ana shirye-shiryen inganta yanayin.

Kafar Daily Post ta Najeriya ta ruwaito cewar, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da izinin gina sabbin gidajen yari shida masu iya daukar mutum 3,000.

Labarai masu alaka