Ana fargabar 'yan ci rani 90 sun nutse tekun Libya

Life jackets washed up on a beach after dozens of migrants drowned in a shipwreck off the Libyan coast of on September 21, 2017 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar tarayyara Turai ta yi kokarin rage yawan 'yan ci rani ta hanyar wata yarjejeniyar da ta kulla da dakaraun da ke tsare gabar tekun Libiya duk da cewar yarjejeniyar ta sha suka

'Yan ci rani 90 ne ake fargabar cewar sun nutse bayan wani kwale-kwale ya kife kusa da gabar tekun Libiya, in ji hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da 'yan gudun hijira.

Mutum uku da suka tsira sun ce yawancin wadanda suka nutse din 'yan kasar Pakistan ne.

An shafe shekaru ana amfani da Libiya a matsayin wata babbar hanyar da 'yan ci rani masu son zuwa Turai ta teku ke bi.

Kasashen kungiyar tarayyar Turai sun yi ta ce-ce-ku-ce game da rage yawan 'yan ci rani da kuma kasashen da ke da alhakin kula da 'yan ci rani in sun iso.

Kungiyar Tarayyar Turai ta kulla wata yarjejeniya da dakarun da ke kiyaye gabar tekun Libiya a shekarar da ta gabata domin taimakawa wajen kama bakin haure tare da mayar da su Libiya.

Amma kungiyoyin bayar da agaji da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun zargi gwamnatoci da daukar matakai na rashin tausayi akan matsalar.

Hakkin mallakar hoto AFP

Mene ne abin da ya faru a hatsari na baya-bayan nan?

Mutum uku ne kawai aka ce sun tsira daga cilkin jirgin kwale-kwale dake dauke da mutum sama da 90. Biyu daga cikin mutanen sun koma gabar teku ta hanyar linkaya, yayin da wani kwale-kwalen masunta ya tsinci mutum na uku.

"Rahotanni sun ce gawarwaki 10 ne ruwa ya tura gabar tekun Libiyan," in ji hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da 'yan gudun hijira (IOM).

Sai dai kuma sabanin yadda aka saba gani, an sami 'yan Libiya uku a cikin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka tsira daga hatsarin kwale-kwalen kamar yadda wakiliyar BBC a arewacin Afirka, Rana Jawad ta ruwaito.

Gawarwakin sun fito bakin teku ne a birnin Zuwara. Shafin Facebook na hukumar tsaro na birnin ya ce wata 'yar Libiya ta nutse yayin da biyu daga cikin wadanda suka tsira suka kasance 'yan Libiya.

Mene ne sabon abu game da kasar da mutanen suka fito?

Galibi irin wannan lamarin na faruwa ne da 'yan ci rani wadanda suka fito daga kasashen bakaken fata na nahiyar Afirka.

A wannan karon kuwa, yawancin wadanda suka kasance a cikin kwale-kwalen 'yan kasar Pakistan ne. IOM ta ce ana samun karin irin wannan yanayin.

Yayin da 'yan kasar Pakistan suka kasance na 13 daga cikin 'yan ci ranin da ke son su isa Turai a shekarar da ta gabata, a halin yanzu dai 'yan kasar ne na uku a wannan shekarar, in ji, IOM.

Labarai masu alaka

Karin bayani