An yankewa maharin masallacin London daurin rai-da-rai

Darren Osborne Hakkin mallakar hoto MET POLICE

An yanke wa mutumin da ya kutsa da mota cikin cinkoson Musulmai a masallacin da ke kusa da arewacin London hukuncin daurin rai-da-rai.

An sami Darren Osborne mai shekara 48 da laifin kashe Makram Ali mai shekara 51, bayan da ya kutsa cikin musulmai da gangan a masallancin Finsbury Park a watan Yunin bara.

A sanadin wannan harin ne Makram Ali ya rasa ransa, kana wasu mutum tara sun sami rauni.

A lokacin da ta ke yanke hukunci, Alkali Cheema-Grubb ta shaida wa Osborne cewa, 'Abin da ka aikata harin ta'addanci ne, kuma ka yi aniyar kashe rayuka ne'.

Shi dai Osborne mutumin birnin Cardiff ne.

Iyalan Mista Makram Ali sun ce ba zasu iya bayyana takaicin da suka ji a lokacin mutuwar ta sa ba.

Da take magana a wajen kotun, 'yarsa Ruzina Akhtar ta ce, 'Babanmu kamar sauran wadanda ta'addanci ya rutsa da su, ba shi da alhaki ko kadan kuma mun ji zafin mutuwarsa ta wannan hanyar'.

Ta kara da cewa, 'Shi mutum ne mai son zaman lafiya, ba ruwanshi da kowa, kuma baya nufin kowa da mugunta'.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption An kashe Makram Ali, mai shekara 51 a yayin harin na masallacin Finsbury

Osborne ya kutsa kan masallata a cikin masallacin Finsbury Park a watan Yunin bara, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Mista Ali da kuma jikkata wasu.

Osborne magidanci ne mai 'ya'ya hudu, ya furta kalaman "Ubangiji ya yi muku albarka, na gode" a yayin da ake tafiya da shi kurkuku.

Labarai masu alaka