Hotunan Afirka: Wanda ya fi tsayi a duniya ya hadu da wacce ta fi gajarta

Wasu muhimman abubuwan da suka faru a nahiyar Afirka da kuma abubuwan da suka faru da 'yan Afirka a fadin duniya cikin wannan makon.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata 'yar Senegal ta mayar da hankali a wata makarantar Firamare a wajen babban birnin kasar, Dakar. Kasar tana taron kasa-da-kasa a wani bangare na wani shirin biliyoyin daloli na shigar da karin kananan yara makaranta a kasashe masu tasowa.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Najeriya sun yi fushi bayan wata 'yar jarida 'yar Faransa ta yi tambaya a farkon makon nan kan ko suna da kantunan littatafai. Kamar yadda wannan hoton na Jazz Hole a Lagos ya tabbatar, lallai suna da su.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A kasar Kenya ranar Talata, dubban mutane sun hallara domin su ga yadda Raila Odinga ya rantsar da kansa.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A wannan rana ce dai kuma likitoci a Alggiers babban birnin Aljeriya, suka fito kan tituna a wani bangare na zanga-zangar wata biyu kan tursasa mutane yin aikin gwamnati.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kwanaki kadan bayan nan ne kuma matar da tafi kowa gajarta a duniya Jyoti Amge 'yar Indiya ta hadu da mutumin da ya fi kowa tsawo Sultan Kosen daga Turkiyya, suka hadu a Masar inda suka dauki hoton da ba a saba samun damar yin haka ba.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A Tunisia, mutane na turuwar yin hoton selfie da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, wanda ke ziyara a kasar.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A Afirka Ta Kudu ma an yi ta turuwar yin selfie da shahararren dan wasan tseren nan Usain Bolt a Johanesburg, a ranar Litinin.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Meftah Taqtaq na kasar Libya ya nufo Zakaria Hadraf na Morocco a lokacin da suke kara wa a wasan zakarun kasashen Afirka tsakanin Morocco da Libya a matakin kusa da karshe , a filin wasa na Mohammed V Casablanca.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wata mata na wucewa ta gefen tekun lokacin faduwar rana a Grand Bassam, da ke Ivory Coast.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata ya fito ya haske kan tsaunin Kadam a garin Nakapiripirit da ke arewa maso gabashin Uganda

Labarai masu alaka

Labaran BBC