Yadda Facebook ya hada wasu Hausawa aure
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Adikon Zamani: Yadda Facebook ya hada wasu Hausawa aure

Ku latsa alamar hoton da ke sama don sauraron cikakken shirin tare da Fatima Zahra Umar:

"Matar mutum", a cewar masu iya magana, "kabarinsa".

Na san wadanda ba su taba haduwa ba, balle su san juna, amma sakamakon abota a shafin sada zumunta na Facebook Allah Ya kaddari su yi soyayya su kuma yi aure za su ce wannan haka yake.

A wannan makon shirin ya duba yadda shafukan sada zumunta ke haddassa soyayya da aure a tsakanin maza da mata.

Na zanta da wasu ma'aurata wadanda suka hadu a dalilin facebook su ka fara soyayya.

Sun yi shekara su na abokantaka a Facebook kafin su hadu a zahiri su ka fada kogin soyayyar juna har abu ya kai ga aure da samun zuri'a.

Sun fada mun cewa babu wani bambanci tsakanin auren da aka saba yi da kuma auren da Facebook ya yi dalilin sa.

Suma suna fuskantar matsalonlin aure amma abun da ya fi muhimmanci shi ne yarda da fahimtar juna.

Wasu kuma ba su samu wannan sa'ar ba. Wata baiwar Allah ta shaida mun cewa ta hadu da wani saurayin da ya yaudare ta a Facebook.

Ta bayyana mun cewa ta fara soyayya da shi ta sakonni ko chat a shafin Facebook.

Shi saurayin ya ce mata shi dalibi ne a wata jami'a a kasar Turkiyya.

A kwana a tashi shakuwa ta karu tsakanin su har suna bayyana wa juna sirrukan da ke zukatansu.

Wata rana ya ce mata ba shi da kudin biyan bukatar makaranta, ya roke ta ta tallafa masa.

Haka ta fara aika masa kudi kullum sabuwar bukata.

An yi shekara daya ana haka kwatsam sai ga hotunan aurensa a shafin Facebook da Instagram.

Ta shaida mun cewa a shekara daya da su ka yi soyayya a Facebook ba su taba haduwa a zahiri ba.

Ta yi bincike kuma bincike ya tona masa asiri; ashe yana nan a unguwar shanu a Kaduna ba Turkiyya din da ya je!

Shawarar wannan baiwar Allah ga 'yan mata masu soyayya a Facebook da samari shi ne: ki maida hankali a kan labaran da zai baki kuma ki tabbata kin hadu da shi a zahiri.

Toh shin za ki iya auren namiji idan kika hadu da shi a shafin sada zumunta?

Labarai masu alaka