Yaran da aka musanyawa iyaye tun suna jarirai

Yaran da aka musanyawa iyaye tun suna jarirai

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon yadda abun ya faru:

Ga wani labari mai sosa zuciya wanda kamar an samo shi daga fina-finan Bollywood ne.

Labarin wasu yara biyu ne 'yan Indiya a garin Assam da aka haifa a asibiti daya, kuma a rana guda.

A sakamakon wani kuskure, ma'aikatan asibiti sun mika su ga mabanbantan iyalai.

Yaran - daya iyayensa Hindu, dayan kuma iyayensa musulmai ne - kuma yanzu shekarunsu uku da haihuwa.

Ma'aikatan asibiti sun amince da sun yi kuskure, kuma an tabbatar da haka ta gwajin kwayoyin halittarsu, amma iyayen nasu sun ce ba za su yarda su musanya yaran ba.