Nigeria: Yadda mota ta kone da 'yan makaranta a cikinta

school bus catch fire for trademore estate
Bayanan hoto,

Motar kenan da ta kone da 'yan makaranta a cikinta

Mazauna unguwar Lugbe dake Abuja na cikin damuwa bayan da wata mota ta kama da wuta, inda har 'yan makaranta biyu suka mutu a sanadiyyar gobarar.

'Yan makarantar na karatu ne a makarantar Je'nisi Little Drops International Academy.

Daya daga cikin yaran kuma ya sami mummunar kuna, kuma an garzaya da shi babban asibitin kasa na Abuja.

Wani mahaifin yara uku da suka tsira da rayukansu, Mista Ekpeyong ya ce 'ya'yan nasa sun sanar da shi cewa man fetur ne ya kare a cikin motar a yayin da suke hanyarsu ta komawa gida daga makaranta.

Sun sanar da shi cewa matukin motar ya tsaya a hanya ya sayi man.

Ya kuma ce yaran nasa sun ce da suka sauke wasu yara a layin Bamaga Tukur ne sai motar ta tsaya.

Daga nan sai matukin motar ya kira mai makarantar ta waya, shi kuma ya zo ya same su tare da makanike.

Yaran na zaune cikin motar a yayin da makaniken ya fara gyaran motar, kuma ba da jimawa ba sai ta kama da wuta.

Yaran sun rika kururuwa suna ficewa daga cikin motar mai daukar mutum 16, amma wasu daga cikinsu hayaki ya turnike su a cikin motar basu sami fita ba.

Bayanan hoto,

Motar ta kone kurmus

Wani wanda ya shaida lamarin da idonsa, Mista Izuka Ejoh ya ce ranar Alhamis ne da yamma abin ya faru.

Ya kuma ce da suka ga motar ta kama da wuta, sai suka garzaya wurin, inda suka tambayi matukin motar ko akwai saurin yara a motar, amma sai ya ce musu babu.

Daga nan ne suka yi ta kokarin kashe wutar, amma daga baya sun ga abin tashin hankali bayan da wutar ta mutu, domin sai kawai suka ga gawar yara biyu a cikinta suna rungume da junansu.

Bayanan hoto,

Sai da makwabta suka taimaka sannan aka iya kashe gobarar.

Rahotanni sun ce matukin motar ya tsere, amma 'yan sanda sun kama mai makarantar, kuma a halin yanzu an rufe ta.

Sauran makarantu dake yankin basu bude ba domin nuna jimaminsu ga halin da yaran wannan makarantar suka shiga.