An rufe matatar mai ta Kaduna

oil refinery Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kamfanin NNPC ya bada sanarwar rufe matatar mai ta Kaduna saboda wasu gyare-gyare da ta ke bukata.

A wata sanarwa da Kamfanin na NNPC ya fitar a Abuja, kamfanin y ace an yi hakan ne domin rashin danyen mai da matatar za ta tace.

An rufe matatar ne a yayin da dama ake fama da karancin man fetur a wasu sassa na kasar musamman arewa maso yamma.

Wakilin BBC ya ziyarci matatar, inda ya leka ofishin kungiyar matuka motocin dakon man fetur, PTD dake harabar matatar man.

Adurraheem Haruna 63, wanda shi ne shugaban kungiyar ya shaida wa BBC cewa ba a ruge matatar da wata mummunar manufa ba.

"An rufe matatar ne saboda injunanta sun gaji, saboda haka tana da shirin a sabunta su"

Ya kara da cewa kuma "Gwamnati ta bayar da umarnin a fitar da man fetur da ake ajiye wa domin bacin rana domin kawo sauki ga al'ummar jihar Kaduna da kasa baki daya."

Amma wasu masu kula da al'amura suna ganin rufe matatar man zai iya ta'azzara lamura.

Abubakar Pele zangon Daura ya ce, "bai kamata ba a bayyana rufe matatar man kamar yadda aka yi. Da an yi abin ta cikin gida, domin wannnan labarin zai kara dagula lamura ne kawai".

Matatr man ta kaduna dai ta sha samun koma baya a ayyukanta a shekarun baya, kuma babu tabbacin ranar da za ta koma bakin aiki.