India: Principal ta horar da dalibai da wuta

An haramta horo mai tsanani a makarantun India Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An haramta horo mai tsanani a makarantun India

'Yan sanda a India sun shigar da karar wata Principal da ake zargi da tursasa wa wasu dalibai 13 dora hannunsu a saman wutar kyandir.

Principal din mai suna Sushanti Hembrom, ta yi kokari ne domin gano ko daya daga cikin daliban wadan da shekarunsu ba su wuce tara ba, ya dauki kudin wani abokin karatunsu.

Wannan lamari dai ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata a wata makaranta da ke jihar Jharkhand, a gabashin kasar ta India.

An dakatar da ita daga aiki ne, bayan iyayen yaran sun kai korafi.

'Yan sandan sun ce, principal din ta ce, ta yi wa daliban hukuncin ne ko da wanda ya dauki kudin a cikinsu zai ji tsoro ya fito da kansa.

Wasu daga cikin yaran sun kone a hannunsu saboda zafin wutar kyandir din, inda daya daga cikinsu ya samu raunin da har aka kwantar da shi a asibiti.

Tuni dai Ms Hembrom, ta amsa laifinta, tare da nadama a kai ta na mai cewa ta aikata ba dai-dai ba, kuma zata nemi afuwar iyayen yaran da ma su kansu daliban.

An dai haramta hukunci mai tsanani da zai cutar da dalibai a makarantun kasar India, amma kuma har yanzu ba a daina ba.

Labarai masu alaka