Pete Souza: Na dauki Obama hoto sau miliyan 2

An nada Pete Souza a matsayin babban mai daukan hoto na fadar White House a watan Janairun 2008, bayan da ya shafe shekaru hudu yana daukar hotunan Barack Obama a lokacin yana dan majalisar dattawan Amurka daga jihar Illinois.

Mista Souza ya rika daukan kimanin awa 10 zuwa 12 kullum tare da Mista Obama, a wasu lokutan ma ya kan yi aiki na kwanaki bakwai a kowane mako.

Ya dauki hotunan Obama kusan miliyan biyu a cikin shekaru takwas na mulkin tsohon shugaban kasar.

Ya ce: "Na lura cewa daukar hotunan shugaban kasa wani aiki ne mai cin lokaci matuka, amma muhimmin aiki ne da yake tabbatar da tarihi."

Ya kara da cewa. "Aiki ne da babu hutu, babu ko da hutu na rashin lafiya, wanda kuma a kodayaushe wayar hannunka ke kunne domin ana iya kiranka babu zato"

Ga wasu hotunan da Pete Souza ya dauka a wancan lokacin, inda ya nuna tsohon shugaba Obama a matsayin mutum mai son wasa, amma kuma mai son aiki tukuru. Ya kuma nuna shi a matsayin mutum mai matukar son iyalinsa da son haduwa da mutanen da yake jagoranta.

Obama kisses Michelle in a lift Hakkin mallakar hoto Pete Souza

Ranar 20 ga watan Janairun 2009, a hanyar tsohon shugaba Obama ta zuwa wajen bikin rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Amurka. Ana iya ganin yadda Obama ya saka wa matarsa Michelle rigarsa ta kwat domin ta ji dumi.

"Sun sami wasu mintuna suna tare da juna tamkar babu kowa a wurin, kuma jami'an tsaronsa sun yi ta kokarin kau da idanunsu daga wannan abin na tsakanin miji da matarsa," inji Souza.

A wannan hoton na kasa ana iya ganin Obama na gyaran kwalar rigarsa a kan hanyarsa ta komawa gida bayan da aka kammala bikin.

Obama ties his bowtie Hakkin mallakar hoto Pete Souza
Obama at a basketball game Hakkin mallakar hoto Pete Souza

Cikin hotunan Mista Obama, akwai wannan na sama da yake nuna halayyarsa ta kula da iyalinsa. Ya halarci wani wasan kwallon kwando da 'yarsa Sasha ta buga a makarantarsu.

"Shugaban kasar da wani mai masa hidima, Reggie Love ne suka tsayawa kociyoyi biyun da basu sami zuwa wasan ba," inji Mista Souza. "Kuna iya ganinsu a yayin da ake wasan tare da sauran 'yan kungiyar Sasha."

A hoto na kasa kuwa, Mista Obama ne tare da 'ya'yan nasa sasha da Malia a cikin dusar kankara yayin da ake wata gagarumar guguwar da ta jibge tarin dusar kankara a Amurka.

Obama plays in the snow with his children Hakkin mallakar hoto Pete Souza
Obama looks through a window Hakkin mallakar hoto Pete Souza

A wannan hoton na sama kuwa, Obama ne yake gaisawa da wasu yara da ke wata makarantar kananan yara da ke Bethesda ta jihar Maryland a Amurka.

Ya ziyarci makarantar ne saboda bikin karshen shekara na makarantar 'yarsa Sasha, inda ya hango yaran na lekensa ta wata taga.

Ban da wadanan yaran ma, Obama na da wasu masoyan, kamar Thelma "Maxine" Pippen McNair. A hoto na kasa ana iya ganinsa tare da matar bayan da ya karrama wasu yara Amurkawa da wani harin bam ya rutsa da su a shekarar 1963 a cocin Sixteenth Street Baptist Church da ke birnin Birmingham na jihar Alabama.

Misis McNair mahaifiyar daya daga cikin yaran da suka mutu a harin bam din ne.

Obama kisses a women in a wheelchair Hakkin mallakar hoto Pete Souza
Angela Merkel gestures to Obama Hakkin mallakar hoto Pete Souza

Hoto na sama kuma na nuna tsohon shugaba Obama ne tare da shugabar Jamus, Angela Merkel a wajen taron kasashen duniya bakwai masu karfin tattalin arziki, wato G7.

Shugabannin sun shaku sosai a shekaru takwas din da Obama ke mulkin Amurka.

Obama and a child Hakkin mallakar hoto Pete Souza

Mista Souza kuma ya dauki hotuna masu yawa a yayin da Obama ke wasa da yara.

A hoto na sama, ana iya ganin Obama na wasa da Ella Rhodes, wadda 'yar mai ba shugaban kasar Amurka shawara kan batutuwan tsaro ce.

Obama ya taba ziyartar gidan sarautar Ingila, Kensington Palace, inda har yayi wasa da jikan gidan Yarima George mai jiran gadon sarautar kasar kamar yadda ake iya gani a hoto na kasa.

Obama meets Prince William Hakkin mallakar hoto Pete Souza
Obama sits at his desk Hakkin mallakar hoto Pete Souza

Obama: Hotunan mutumin da ba kowa ya sani ba, wadanda Pete Souza ya wallafa.