South Africa: Dukkan mahakan ma'adinai 955 sun tsira

A rescued South African miner gestures out a bus window, 2 February 2018 Hakkin mallakar hoto AFP / Getty Images
Image caption Daya daga cikin wadanda aka ceto daga cikin ramin hakar zinare na amsa gaisuwa daga tagar mota

An yi nasarar ceto dukkan masu hakan ma'adinai da suka makale su 955 a Afirka ta Kudu.

Sun makale tun ranar Laraba a karkashin kasa tun da rashin wutar lantarki ya hana injunan da ke fito da ma'aikatan yin aiki.

"Mun ceto kowa da kowa," inji James Wellsted, wanda shi ne kakakin kamfanin Sibanye-Stillwater da ke tafiyar da ayyuka a wurin.

Wakiliyar BBC a Afirka ta Kudu, Pumza Fihlani ta ce ana ta murna bayan da aka fito da ma'aikatan.

Hakkin mallakar hoto AFP/getty
Image caption Power has now been restored at the site An dawo da wutar lantarki bayan kwana 3 ana fama

Afirka ta Kudu ce kan gaba wajen hakar zinare a duniya, amma akwai matsalolin rashin matakan tsare lafiyar ma'aikata.

Ma'aikatan na aiki ne a garin Welkom da yake kimanin kilomita 290 yamma maso kudu daga birnin Johannesburg.

Tana da hawa 23 wadanda suka kai zurfin mita 1,000 a karkashin kasa.

Fiye da mahaka ma'adinai 80 ne suka rasa rayukansu a shekarar 2017 saboda rashin ingancin yanayin kare lafiyar ma'aikata.

Labarai masu alaka