Amurka ta haramta sayar wa Sudan ta Kudu makamai

Sudan ta Kudu ita ce kasar da take da yawan matasa a duniya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sudan ta Kudu kasar ce da ta ke da yawan matasa a duniya

Amurka ta haramta shigar da makamai Sudan ta Kudu ta kuma bukaci sauran kasashe da Majalisar dinkin duniya da su bi sahun haramta cinikin makamai a fadin duniya.

Amurkan ta nuna damuwa da kuma gazawar shugabannin kasar wajen kawo karshen yakin basasar da aka shafe shekara hudu ana yi.

A karshen watan da ya gabata ne, jakadan Amurka a majalisar dinkin duniya Nikki Haley ta bayar da sanarwar Washington ta hakura da cewa Shugaba Salva Kiir, zai iya kawo sauyi, kuma ta kira shi "wanda bai dace" a yi tafiya da shi ba a fafutukar neman zaman lafiya.

"Shugabannin Sudan ta Kudu ba wajen tafiyar da jama'arsu kawai suka gaza ba, har da zaluntarsu". inji sakatariya Haley.

Sudan ta Kudu tana cikin kasashe mafi yawan matasa a duniya, wacce ta samu 'yancin kai a shekarar 2011.

Labarai masu alaka