Syria: An harbo jirgin yakin Russia

Jirgin kirar Sukhoi-25 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin yakin Rasha kirar Sukhoi-25

Rahotanni na cewa an harbo jirgin yakin Rasha kirar Sukhoi-25 a yankin da 'yan tawaye ke rike da ikonsa kusa da birnin Idlib da ke arewacin Siriya.

Wani bidiyon da ke yawo a shafikan sada zumunta ya nuna cewa an harbo jirgin, wani bidiyon kuma ya nuna jirgin na ci da wuta a kasa,

A karshen watan Disamba ne dakarun gwamnatin Siriya suka kaddamar da wani shiri a yankin Idlib, wanda jiragen Rasha ke marawa baya.

Kungiyoyin 'yan tayar da kayar baya da suka hada da na al-Qaeda masu alaka da Hayat Tahrir al-Sham na da karfi a arewa maso yammacin lardin.

Ba a faye samun irin wannan harin ba akan sojin saman Rasha tun lokacin da ta fara gangaminta a Siriya a watan Satumbar 2015.

A watan Agustan 2016 ma an taba kai irin wannan harin, inda dukkanin mutane biyar da suke cikin wani jirgi suka mutu a lokacin da aka harbo shi a Siriya.

Labarai masu alaka