Cutar Daji ta fi kisa a kasashe masu tasowa

A kasashe masu tasowa ne ake samun kashi saba'in cikin dari na mutanen da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A kasashe masu tasowa ne ake samun kashi saba'in cikin dari na mutanen da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar

Wata kungiya mai yaki da cutar daji a duniya ta kiyasta cewa, cutar na kashe mutum miliyan takwas da dubu dari takwas duk shekara, kuma galibinsu a kasashe masu tasowa.

Kungiyar mai suna Union for International Cancer Control, UICC, ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a yayin da ake bikin ranar cutar daji ta Duniya a yau Lahadi.

A cewar kungiyar a kasashen masu tasowa ne, ake samun kashi saba'in cikin dari na mutanen da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar, saboda karancin abubuwan da ake bukata don fuskantar larurar.

"Inda aka fi samun rashin daidato (wajen samar da kayan aikin yakar cutar) shi ne a tsakanin yara - wadanda musamman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar a wani muhimmin rahoto da ta fitar a 2017 cewa kashi 20 cikin dari ne kawai ke warkewa daga cikinsu a kasashe marasa galihu, sabanin kashi 80 cikin dari a kasashen da suka ci gaba", inji sanarwar.

An dai ware ranar 4 ga watan Fabrairun ko wacce shekara a matsayin Ranar Cancer ta Duniya don samar da wani dandamali da al'ummar duniya za su hadu su yi musayar ra'ayi game da hanyoyin yaki da cutar daji.

Hakkin mallakar hoto uicc.org
Image caption Farfesa Sanchia Aranda

Bikin ranar na bana na zuwa ne a daidai lokacin da aka shiga shekara ta karshe ta wata yekuwa da aka kaddamar don duba hanyoyin da kowa -- a daidaiku ko a kungiyance -- zai taka rawa don rage larurar daji a duniya.

Taken yekuwar ta shekara uku wadda aka kaddamar a 2016 shi ne "Za mu iya. Zan iya".

Sai dai ko da yake ba ta bayyana nasarar da aka samu a wannan yekuwa ba, kungiyar ta UICC ta yi fatan samun daidaito wajen samar da abubuwan da ake bukata don tunkarar cutar.

Sanarwar ta ambato shugabar kungiyar, Farfesa Sanchia Aranda, tana cewa, "A wannan shekara ta karshe ta yekuwar "Za mu iya. Zan iya" ana fatan zaburar da gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu don tabatar da daidaito a tsakanin masu shi da marasa shi wajen bincike don gano cutar, da samar da magunguna, da kuma kula da masu larurar, wacce ta fi shafar marasa galihu a cikin al'umma a ko wacce kasa".

Sannan kungiyar ta yi kira da a kara zage dantse don ganin an cimma burin hukumar lafiya ta MDD, WHO, na rage mutuwa sanadiyyar cututtukan da ba a yada su da kashi 25 cikin dari nan da shekara ta 2025, burin da ta ce za a iya cimmawa.

A cewar Farfesa Aranda, "Burin Hukumar Lafiya ta Duniya, wanda aka kaddamar a 2011, na rage mutuwa sakamakon kamuwa da cututtukan da ba a yada su da kasi 25 cikin dari a shekara 14 ya kusa zuwa zango na tsakiya. Za mu iya cimma wannan burin, amma ana bukatar jajircewa fiye da da."

Labarai masu alaka