Mexico: An kama 'yan ci rani 200 a Mexico

Police instruct a group of Central American migrants intercepted as they crossed the country in the Tamaulipas state, Mexico, 3 February 2018 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Maza da mata da yara ne ke makare cikin motar

An gano kusan 'yan ci rani 200 makare cikin wata motar daukan kaya a arewa maso gabashin Mexico.

Mutanen da suka hada da maza da mata da kananan yara, an same su a cikin motar ne a jihar Tamaulipas da ke kudu da iyakar kasar da da jihar Texas ta Amirka, inji jami'an gwanatin yankin..

'Yan ci ranin sun fito ne daga kasashen Guatemala da Honduras da kuma El Salvador, kuma suna kan hanyar zuwa Amirka ne.

An kama mutum uku da ake tuhuma da laifin safarar mutane.

Jami'an 'yan sandan Mexico sun bayyana yadda aka gano 'yan ciranin.

Sun ce an tsayar da motar ne a wani shingen duba motoci, kuma aka yi amfani da na'urar duba kaya, inda aka tabbatar da akwai mutane a cikin motar.

An gane cewa mutanen basu da abinci ko ruwa, kuma 24 cikin su ba su da yara tare da su.

Kassshen Guatemala da Honduras da kuma El Salvador ne suka fi samar da 'yan ci ranin da basu da izinin shiga Amirka a kowace shekara.

Labarai masu alaka