'Yan ci rani: An gano gawa 20 a teku kusa da Morocco

African migrants at sea Hakkin mallakar hoto AFP

An tsamo gawar mutum akalla 20 daga tekun Bahar Rum kusa da gabar tekun Melilla da yake karkashen ikon Spaniya a kan iyaka da Morocco.

Sojojin ruwa na Morocco ne suka tsamo gawarwakin bayan da ma'aikatan wani jirgin ruwan fasinja suka hango su a ruwa.

Ana tsammanin \yan ci rani ne daga kasashen Afirka, daga yankin yamma da hamadar Sahara.

Ana tsammanin 'yan ci ranin na kan hanyarsu ta tsallaka tekun Bahar Rum ne domin isa Turai.

Kuma ana ganin sun so su isa Melilla ne, duka da cewa an sanar da mazauna yankin cewa akwai yiwuwar samun guguwa mai karfi a wannan lokacin.

Melilla na da girman kilomita 12 ne kawai, kuma wuri ne da 'yan ci rani ke amfani da shi wajen tsallakawa zuwa Turai don neman aikin yi ko mafaka.

Wannan yankin - da na Ceuta wanda shi ma yana karkashin mulkin Spaniya ne - shi ne ke da iyakar doron kasa tasakanin Turai da Afirka.