Kaduna: Zaki ya kufce daga gidan Zoo

African lion in a zoo Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Asabar mutane da ke zuwa filin shakatawa na Gamji Gate a Kaduna suka tsallake rijiya da baya bayan da wani zaki ya kufce daga inda ake tsare da shi.

Majiya daga filin shakatawar ta Gamji Gate ta shaida wa wakilin BBC cewa Zakin ya kufce ne yayin da daya daga cikin masu kula da shi ke bashi abinci.

Rahotanni sun ce Zakin ya yayyaga shi, ya kuma sami nasarar ficewa daga wurin da ake tsare da shi.

An yi ta gudu a filin na Gamji bayan da masu shakatawa su ka tsinkayi Zakin.

Wadanda suka shaida lamarin da idonsu sun kuma bayyana wa BBC cewa Zakin da kan sa ya koma cikin inda aka killace shi ba tare da ya kassara wani mutum ba.

Filin shakatawa na Gamji a Kaduna na da karamin wurin ajiye namun daji wato, Zoo kuma akwai Zaki, da Jimina, da wasu Birai, Bareyi da kuma Kuraye.

Akan zargi masu killace irin wadannan namun daji da barin su cikin yunwa, abinda watakila ya sa su ke tunzura har su yi kokarin kufcewa.

Wakilin BBC, Nura Ringin ya ce, "Ranar Laraba da na shiga Gamji Gate babu shakka na ji Zaki na ta gunji."