Ban ce kada a zabi Buhari a 2019 ba - Babangida

Former Nigeria President Ibrahim Babangida Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Babangida ya karyata sanarwar da ke cewa yayi kira ga 'yan Najeriya da kada su zabi gwamnatin Buhari a 2019.

Kalaman tsohon shugaban kasar na cikin wata sanarwar ce wadda PR NIgeria ta fitar, inda ya ke musanta cewa rahotannin ba su yi daidai da kalaman da yayi amfani da su ba a cikin sanarwarsa akan batun.

Tsohon shugaban kasar kuma ya nemi Najeriya ta samar da tsarin jam'iyyun siyasa biyu, wanda a ganinsa shi ne yafi kyau ga kasar.

Shugaban ya ce, "Bayanan da aka fitar a cikin sanarwar da aka danganta da ni ba nawa ba ne."

A cikin sanarwar ta baya-bayan nan tsohon shugaban ya ce, "Babu wani shinge tsakani na da masu rike da madafan iko a Najeriya."

"Saboda haka ba sai na shiga kasuwa ba a duk lokacin da wata matsala ta dame ni, inji shi.

Da farko dai an sami wata sanarwa da ta fito ta kafofin watsa labarai cewa tsohon shugaban ya yui kira ga shugaba Muhammadu Buhari da kada ya tsaya takara a 2019.