Jirgin kasa sun yi arangama da juna

Sama da mutum 70 ne suka jikkata Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sama da mutum 70 ne suka jikkata

'Yan sanda sun ce wani jirgin kasa mai dauke da mutum 147 ya yi karo da na daukar kaya a jihar Carolina ta kudancin Amurka, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu.

Sama da mutum 70 ne suka jikkata a cikin jirgin da yake zirga-zirga tsakanin New York da Miami.

Al'amarin ya faru bayan kwana hudu da wani direban mota ya rasu a lokacin da motar da yake tukawa ta yi arangama da wani jirgin kasan da ya dauko 'yan majalisar Amurkan a cikin jihar Virginia.

Tuni hukumar bayar da agaji ta Amurka ta tura masu aikin ceto, kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta ce an zakulo dukkan fasinjoji daga cikin jirgin.

A cewar Amtrak, fasinja 139 ne da ma'aikata takwas a cikin jirgin.

Sai dai ba a san adadin mutum nawa ne a cikin jirgin dakon kayan ba.

A ranar Laraba ma, mutum shida ne suka jikkata a lokacin da wani jirgin kasa da ya dauko 'yan majalisar jam'iyyar Republican suka yi karo da wata babbar mota.

A cikin jirgin har da kakakin majalisar dokokin Amurka, Paul Ryan, kuma hatsarin na Virginia ya yi sanadiyyar mutuwar direban motar.

Labarai masu alaka