'Gwamnan Zamfara 'ya san mutanen da ke kai hari a jiharsa'

Gwamna Abdul'aziz Yari Hakkin mallakar hoto PreMIUM TIMES

Wani dan majalisar dattawan Najeriya ya yi zargin cewa gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari ya san 'yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar amma ya ki daukar mataki a kansu.

Sai dai gwamnatin jihar ta ce wannan zargi ba shi da kanshin gaskiya.

Sanata Kabiru Marafa ya shaida wa BBC cewa masu satar shanu sun kashe kusan mutum 1400 a jihar ta Zamfara cikin shekara biyar amma babu wani mataki takamaimai da gwamnatin jihar ta dauka domin shawo kan lamarin.

A cewarsa, "Lokacin da aka yi kashe-kashe a jihar Benue, gwamna jihar ya tattara dukkan masu masu abin cewa a jihar, an zauna da su har abin ya zama batun tattaunawa a kai domin suna ganin bai kamata a ci gaba da kashe mutanesu ba. Me ka taba ji an yi a Zamfara?

"Yanzu sai mu zauna babu wanda zai yi magana; kullum abin da kake ji shi ne 'an kashe wane, an sace wane'. An ki magana saboda kawai ana jin tsoron gwamna."

Sai dai Kwamishinan kananan hukumomin jihar, Alhaji Bello Dankande, ya gaya wa BBC cewa kalaman dan majalisar ya yi na cike da kura kurai.

"Kure ne babba ga dan majalisar a matsayinsa na dan jihar Zamfara ya je majalisa ya fadi cewa gwamna da mataimakinsa da kuma gwamnatinsa sun san abin da yake faruwa na rashin tsaro a jihar.

"Al'umar jihar Zamfara da sarakuna da kuma jami'an tsaro shaidu ne kan kudin da aka kashe domin wanzar da tsaro. Don haka ba zai yiwu a ce ana kashe wadannan makudan kudade domin tabbatar da tsaro ba, amma a ce Gwamna Abdul'aziz Yari ya san abubuwan da ke faruwa."

Ya kara da cewa siyasa ce ta sa dan majalisar dattawan yin kalaman, yana mai yin kira a gare shi da ya rika "yin abubuwan da suke na daidai."

Labarai masu alaka