Ganduje ya gayyaci makiyaya su koma jihar Kano

Abdullahi Umar Ganduje Hakkin mallakar hoto KANO STATE GOVERNMENT
Image caption Gwamna Ganduje ya ce akwai filayen kiwo a Rogo da Gaya da Kura da Tudun Wada da Ungoggo.

Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya gayyaci Fulani makiyaya su koma jiharsa domin gudanar da kiyo ba tare da samun matsala ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Lahadi lokacin da yake kaddamar da yin allurar rigakafin cutukan dabbobi a karamar hukumar Garun Mallam.

Ya ce jiharsa tana da isassun filayen noma da kiyo ga kowanne makiyayi da manomi.

A cewarsa, idan makiyayan suka amsa gayyatarsa za a kaucewa rikicin manoma da makiyaya musamman wanda ke faruwa a jihohin Benue da Taraba.

Rikicin, wanda ya yi sanadin asarar rayuka daga dukkan bangarorin biyu, ya jawo hankalin kusan daukacin 'yan Najeriya.

Gwamnatin tarayya dai ta yi kira ga gwamnonin jihohin da lamarin ya shafa su samar da wuraren kiwo.

Sai dai gwamnonin sun yi fatali da wannan kira, suna masu cewa ba su da isassun filayen da za su bayar domin yin kiwo.

Amma Gwamna Ganduje ya ce "Ina gayyatar makiyaya daga dukkan fadin Najeriya zsu komo jihar Kano saboda muna da isasun filayen kiwo. Muna da wuraren kiwo a kananan hukumomin Rogo da Gaya da Kura da Tudun Wada da Ungoggo da sauran wurare, inda za mu ba su su gudanar da ayyukansu."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana zargin Fulani da kashe-kashe, sai dai sun musanta.

Labarai masu alaka