Buhari ya amince a fifita 'yan Nigeria kan 'yan kasar waje

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince a rika bai wa 'yan kasar fifiko kan 'yan kasashen waje wurin bayar da kwangiloli.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake sanya hannu kan wasu takardun dokar shugaban kasa a fadarsa da ke Abuja.

"A cikin wannan doka ta shugaban kasa, Shugaban ya ba da umarni ga hukumomi da ma'aikatun gwamnati su rika bayar da fifiko ga kamfanonin cikin gida wajen tsarawa da aiwatar da ayyukan tsaron kasa," in ji wata sanarwa da shugaban ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya kara da cewa ya dauki matakin ne domin kara samar da ayyuka ga 'yan Najeriya.

Sai dai ya kara da cewa za a bai wa kamfanonin waje dama idan har kamfanonin cikin gida ba su da kwararrun da za su aiwatar da wani aiki da kwangiloli da gwamnati ke son su yi.

Shugaban ya haramtawa ma'aikatar cikin gida bayar da bisa ga 'yan kasashen wajen da za su shigo Najeriya domin gudanar da dukkan ayyukan da akwai wadanda ka iya yin su a kasar.

Labarai masu alaka