Jirgin ruwa ya bace da ma'aikata 22 a gabar tekun Benin

Map showing Benin, its capital, Porto-Novo, and the Gulf of Guinea

Wani jirgin ruwan dakon man fetur ya bace tare da ma'aikata 22 'yan asalin Indiya a yankin mashigin tekun Guinea da ke Afirka ta Yamma.

Ba a ji duriyar jirgin na Marine Express da ma'aikatansa ba tun ranar Alhamis.

Wannan lamarin ya faru kasa da wata daya da masu garkuwa da mutane suka kama wani jirgin ruwa a yankin.

Hukumomi sun ce sojin kasar Benin na neman jirgin mai suna Maritime Bureau, wanda yake dauke da tan 13,500 na man fetur.

A watan Janairu ma aka sace wani jirgin a daidai wannan yankin amma an sake shi bayan kwana shida a yayin da aka biya kudin fansa.

Ministar harkokin waje ta Indiya, Sushma Swaraj, ta ce gwamnatin kasar na aiki tare da mahukunta a yankin domin gano jirgin.

Jirgin na karkashin kulawar kamfanin Anglo-Eastern na Hong Kong ne.

Wakilin BBC, Will Ross ya ce a da yankin gabar tekun Somaliya ne aka fi sani da wannan lamari mai hatsari, amma bayan da aka tura jiragen yaki na kasa-da-kasa a yankin, lamarin tsaro ya inganta.

A halin yanzu kuwa yankin Afirka ta yamma ke kan gaba wajen fashi da garkuwa da jiragen ruwa.

Labarai masu alaka