Nigeria: Jagoran mabiya Shi'a na Sokoto ya rasu

shia
Bayanan hoto,

Malamin ya rasu ne 'yan makonni bayan da aka harbe shi a kafa yayin da 'yan sanda suka tarwatsa su lokacin da suke wata zanga-zanga a Abuja

Shugaban kungiyar mabiya mazhabar shi'a ta Najeriya reshen jihar Sakkwato ya rasu.

Malam Kasim Umar ya rasu ne da yammacin ranar Litinin a garin Sakkwato, in ji Ibrahim Musa jam'in watsa labarai na kungiyar ta IMN.

Malamin ya rasu ne 'yan makonni sakamakon harbin da mabiya shi'a ke zargin 'yan sanda da yi masa a kafa, yayin da 'yan sandan suka tarwatsa su -- sa'adda 'yan kungiyar suka yi wata zanga-zanga kan halin da shugaban nasu na kasa Malam Ibrahim Zakzaky ya shiga ranar tara ga watan Janairu.

Malam Kasimu dai ya kwashe sama da shekara 20 yana shugabantar gwagwarmayar shi'a a birnin Sakkwato mai rinjayen mabiya sunnah.

Ya kwashe fiye da shekara biyar a daure bisa zarginsa da hannu a kisan wani malamin sunna mai wa'azin nuna kyamar shi'a a Sakkwaton, Malam Umar Hamza Danmaishiyya a shekara ta 2007, amma daga bisani kotu ta wanke shi.