Jacob Zuma: Shugaban South Africa na cikin tsaka mai wuya

South African President Jacob Zuma in the capital, Pretoria, August 19, 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya kafe cewa ba zai sauka daga mukaminsa ba

Kujerar shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu na tangal-tangal a yayin da manyan shugabannin jam'iyya mai mulki ta ANC ke wani taron gaggagwa a birnin Johannesburg.

Ashirin daga cikin shugabannin jam'iyyar ta ANC na duba wa'adin mulkin Mista Zuma, kwana daya bayan da shugaban ya yi biris da kiraye-kirayen ya sauka daga mukaminsa.

Akwai matsin lamba sosai akan Mista Zuma da ya sauka kafin ya gabatar da jawabinsa na shekara-shekara game da halin da kasar ke ciki.

Wa'adinsa zai kare a shekarar 2019.

Shugaba Zuma ya taba zaman kurkuku a lokacin da yake cikin gwagwarmayar yaki da tsarin launin fata, kuma ya gana da manyan shugabannin jam'iyyar su shida amma sun kasa tankwaro shi da ya sauka.

Julius Malema wanda yake adawa da gwamnati ne ya ce Mista Zuma ya ki sauka daga mukaminsa tun da wuri, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Amma wasu rahotannin na cewa Mista Zuma ya nemi kariya daga shari'a ga shi kansa da iyalansa kafin ya amince ya sauka.

Me zai faru nan gaba?

Ya danganta ga abin da manyan shugabannin ANC su ka tsayar a taronsu.

Ana iya kiran babban taron kwamitin gudanarwa mai mambobi 80 domin su yi wa shugaba Zuma kiranye.

Kuma idan suka yi masa kiranye, dole Mista Zuma ya sauka da kashin kansa, kamar yadda wanda ya gada, wato Thabo Mbeki ma ya yi a 2008.


Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe (daga hagu), tare da shugaba Zuma a 2015

Karin bayani

Labaran BBC