Nigeria: Wani matashi na taimakon yara masu rayuwa a kwararo

Wasu daga irin yaran da James Okina (mai bakar kwat a tsakiya) ya taimaka
Bayanan hoto,

Da dama daga cikin yaran da James Okina (mai bakar kwat a tsakiya) ya taimaka sun fito ne daga sansanonin 'yan gudun hijira

A jerin wasikun da muke kawo muku daga 'yan jaridar Afirka, a wannan karon za mu kawo muku wani labari ne daga marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani, wadda ta duba rayuwar wani matashi a Najeriya, wanda yake taimakon yara da ke rayuwa a kwararo a birane.

Wannan matashi James Okina, wanda ya rungumi wannan akida ba ya boye tarihin irin rayuwar da shi kansa ya shiga: Sata a kantuna da satar kayan 'yan ajinsu da guduwa daga makaranta.

A fili Okina yake, bayyana cewa, ''na hadu da miyagun abokai.''

Wannan abu ne mai ban mamaki ganin yadda matashin har yanzu bai wuce shekara goma sha ba, kuma yana shekara ta uku ke nan da yake jagorantar wata kungiya da ya kirkiro mai suna ''Street Priests'' (Masu Wa'azi a Titi), domin taimaka wa tarin yara marassa galihu da ke gararamba a titunan Calabar, babban birnin jihar Cross River, a kudancin Najeriya.

Wannan abu ne da matashin yake dangantawa da mutane biyu da suka taimaka masa shi kansa wajen fito da shi daga waccan rayuwa da shi kansa ya shiga.

Na farko dai shi ne, wani dan uwansa na biyu kuwa shi ne wani yaro dan shekara 13 da ya hadu da shi a wajen wani wasan kwallon kafa a shekarar da ya gama makarantarsa ta sakandare, sanye da kaya marassa kyau, kamar almajiri.

Wannan yaro da ya gani a cikin halin kunci, sunansa Frederick, yana daya daga cikin daruruwan yaran da suke gararambar rayuwa da kula da kansu a Calabar.

Da dama daga cikinsu sun fito ne daga sansanonin da ke kusa da wani gida da ake kula da mutanen da da suka gudo daga muhallansu bayan da Najeriya ta mika yankin Bakassi mai arzikin mai, ga makwabciyarta Kamaru, sakamakon hukuncin kotun duniya.

Wasu daga cikin yaran, iyayensu sun yi watsi ne da su bisa zargin su mayu ne, wanda wannan wata mumunar al'ada ce a makwabciyarsu, jihar Akwa Ibom.

To amma a nan shi Frederick, yana da mahaifiya wadda yake zaune a daki daya da ita, sai dai ta tafi wata takwas da ya wuce, ta bar shi, shi kadai yana kula da kansa.

Okina ya ce, '' idan ka gan shi ba kyawun gani, kayansa kaca-kaca, amma kuma na yi mamakin yadda yake da basira.''

Bayanan hoto,

James yana karatun harkokin kasuwanci ne a jami'a

Kamar sauran yara da suke rayuwa a kwararo, Frederick da abokinsa Kevin suna samun dan abin da za su rayu ne ta hanyar bara da rana. Sannan kuma da daddare abokan 'yan shekara 13, sukan je gidajen rawa da shan barasa suna wasan alkafura mutane na ba su kudi.

Okina ya rika zuwa wurinsu kullum, inda yake zuwar musu da dan abin cin kwalan da makulashe.

Okina ya ce, ''yadda abotarmu ta kullu shi ne, a kan abubuwan da muke tattaunawa a kai, amma ba kudi ko abinci ba.''

''Duk maganar da muka yi, sai na ga cewa lalle akwai nauyin da ya rataya a wuyana a game da su.''

To amma abin shi ne, shi kansa Okina ba shi da wani kudi ko wani abu mai yawa da zai iya taimaka musu, domin a lokacin yana aiki ne a wani shagon sayar da tufafi da sauran kaya, yayin da yake zaman jiran takardarsa ta shiga jami'a.

Burinsa shi ne ya zama dan kasuwa wanda wata rana zai zama sanannen hamshakin attajiri a harkar gidaje.

Bayanan hoto,

Inyang Edem (mai jar riga) - wanda ya fara taimaka wa da kudin da aka kai yaran farko makaranta, tare da Okina

Ya san cewa wadannan yara suna bukatar taimako, saboda haka ya tuntubi wani mutum mai suna Inyang Edem a cocinsu wanda ya yarda ya bayar da taimakon kudi da sauran abubuwa domin tallafa wa Frederick da Kelvin su koma makaranta.

Okina ya ce, ''bayan na mayar da wadannan yara makaranta, na shiga cikin harkar tusundum ke nan.''

Okina ya samu kansa cikin harka da irin wadannan yara na kwararo, inda ya yi abota da wasunsu da ke tattaruwa a wani wuri kusa da gidansu, suna daukar lokaci mai tsawo suna hira kusan a kullum.

Wata rana sun gama hira, ya juya ke nan zai kama hanyar gida, sai daya daga cikinsu ya rikea hannunsa.

Okina ya dauka kudi yaron zai tambaye shi.

''Amma maimakon haka, sai na ji ya ce: 'Kawu, don Allah ka dawo','' In ji Okina.

Daga nan ne kawai sai Okina ya ji a ransa cewa lalle wajibi ne ya tashi tsaye domin taimaka wa yaran nan. Ya ga cewa idan ya samar da wani kyakkyawan tsari zai ba shi damar samun karin tallafi da kuma yadda zai rika tafiyar da aikin da kyau, sai kawai ya fara wa'azi a titi.

Ya ce: ''A lokacin da jama'a ke karkata ga gwamnati da malamai masu wa'azi domin samun sauyi a cikin al'umma, za ka iya bayar da 'yar gudummawarka da dan abin da kake da shi daga inda kake.

Bayanan hoto,

Marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani

Okina ya bayyana cewa: ''Ba wani babban malami da zai kaddamar da kai kafin ka zama mai wa'azi. Wannan ne ya sa ake kiranmu masu wa'azin titi.''

Ta hanyar amfani da shafin Facebook da sauran shafukan sadarwa, Okina ya samo kudin taimaka wa ilimin wasu yaran 15.

Ya ci gaba da ziyartar wasu yaran da ke rayuwa a kwaroro a sauran sassan birnin Calabar, kuma kafin ka ce me, ya zama sananne a wurinsu, inda kusan da sun gan shi a wata mota, tasi ko bas, za su ruga su je wurinsa har sauran mutane da ke cikin motar su rinka jin kamar sun dame su.

Bayan shekara uku, Okina mai shekara 18, wanda a yanzu ya zama dalibi a fannin nazarin kula da harkokin kasuwanci a Jami'ar Calabar, ya samu hanyar samun tallafin daukar dawainiyar yara 215, inda yake da masu bayar da tallafi kusan 50.

Ya ce ba shi da niyyar neman wani aiki, wannan ne aikin da zai dukufa yi har bayan kamala karatunsa na jami'a.

Bayanan hoto,

James ya fara taimakon yara ne tun yana shekara 15

Karfin halinsa a wannan aiki ba wani abin mamaki ba ne, ganin irin wahalar da ke tattare da wa'azin kwararo, wanda ba shi damar ganin irin mawuyacin halin da wasu yara kan samu kansu a ciki.

Misali, akwai yaron da aka kusa yi masa atire ko jefe shi saboda wani dan abu da ya sata, da wani wanda ya kwanta rai-kwakwai-mutu-kwakwai a gefen titi har tsawon sa'a 24 bayan ya bugu da kwaya, da kuma wasu yaran guda uku wadanda tirken wutar lantarki ya fado musu gaba daya ya kashe su.

Sannan ga wani yaron kuma da ya tsira daga matsafa, wanda ga alamar saran adda nan a fuskarsa, wanda mutanen da suka so kama shi suka yi masa, lokacin da suka kai masa farmaki.

Okina ya ce: ''Mutane suna cewa wai yaran da ke rayuwa a kwararo, sun zama gagararr, amma ni ina ganin ba haka ba ne- ba su zama gagararru ba.''

Ya ce: ''Ga yadda yaran kwararo suke zama gagararru. Suna ganin yadda abokansu ke mutuwa. 'Duniya ba ta damu ba, saboda haka me zai sa na damu?''

Okina ya san matsalar yadda za a ce ba wanda ya damu. Ya san abin da ke tattare da wannan rashin damuwa na kowa.

Rayuwarsa ta kwanciyar hankali ta sauya tun yana dan shekara takwas lokacin da iyayensa suka rabu, aurensu ya mutu. Mahaifiyarsa ta bar gidan, amma mahaifinsa ya kafe sai Okina, wanda shi ne dansu na tsakiya ya zauna tare da shi, da kuma 'yan uwansa biyu.

Daga nan sai rayuwarsa ta sauya, ya kasance cikin damuwa da bacin rai, ya zamanto lokacin da yake yi a waje ya fi na zamansa a gida, ya rika mu'amulla da abin da ya kira ''abokan da ba su dace ba''. Ya yi baya a makaranta kuma kusan ko da yaushe yana cikin rikici, ba a ma maganar sata.

Ya ce: ''Na san cewa wannan ba halina ba ne amma ba wanda zai cece ni daga rayuwar.''

''Al'umma tana da saurin bayyana mutum a matsayin bata-gari. Mutane ba sa kallon wanda zai gaya musu cewa, abin da suke yi bai daidai ba ne. Suna neman wanda zai taimaka musu ya fitar da su daga irin wannan rayuwa.''

Allah cikin ikonsa Okina ya samu taimako: Wani dan uwansu daga Legas ya karfafa wa matashin guiwa.

Okina ya ce, wannan dan uwa nasu, yakan je wajen matasa da ke makarantar sakandare da kuma bariki a Legas da littattafai ya ba su suna karantawa, ''wannan ya karfafa min guiwa. Mutum ne mai tunani da hangen nesa da kuma ilimi.'' In ji shi.

Ta hanyar saurare da kuma tattaunawa da wannan dan uwa nasu, sai Okina a hankali ya sauya rayuwarsa. Ya fara mayar da hankali sosai a kan karatunsa, nan da nan ya koma matsayinsa na daya a ajinsu.

Bayanan hoto,

Okina, wanda ke jawabi ga wasu yara da ke rayuwa a kwararo, yana fatan fadada ayyukan kungiyarsa

Okina ya ce, yawancin mutanen da suke bayar da taimako ga kungiyarsa a yau, 'yan ajinsu ne, wadanda suka san yadda yake yana dalibi, da kuma yadda ya sauya ya zama na gari, ba zato ba tsammani.

Ya ce: ''Suna gaya wa yaran irin yadda rayuwata ta kasance kuma labarin nawa na karfafa musu guiwa.''

Babarsa ita ma tana bayar da gudummawarta, inda take koyar da yaran darasin harshen Ingilishi kyauta. Babansa kuma ya mutu a shekarar da ta wuce.

Kungiyarsa ta fadada aikinta daga nema wa yara masu gararamba a kwararo hanyar samun ilimi, ta hada da yaran da ke cikin hadarin kaiwa ga rayuwa a titi, kamar wadanda suke sansanonin 'yan gudun hijira.

Aikin kungiyar yanzu ya hada da neman 'yancin yara, da fadakar da mutane kan 'yancin yara da kuma samar da rayuwa ta gari ga yara.

Wannan ya kasance mafi wahala, kasancewar mutane ba sa son bayar da hayar wurinsu domin gudanar da wani taro da ya shafi yara masu rayuwa a kwararo.

A kan haka ne, Okina ya ce shirinsa yanzu shi ne su mallaki wuri nasu na kansu.

A watan Disamba na 2017 kungiyarsa ta yi wani taro domin nuna godiya da girmama wadanda suka yi fice wajen ba su gudummawa da sauran taimako.

Edem, wanda ya ba wa Okina kudin da ya mayar da Frederick da Kelvin makaranta, ya samu kyauta ta musamman, abin da ya sanyaya zuciyarsa har sai da ya zubar da hawaye.

A lokacin da ya bayar da kudin, bai yi tunanin cewa ya fara wani abu ne da ya zama wani abin da ya zama a yau ba(na alheri), in ji Okina.