Kasuwar Hannayen jarin Amurka ta fadi

Amurka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A rana daya Hannayen Jarin Amurka sun yi faduwar da ba a taba gani ba a shekaru da dama

Kasuwar hannayen jarin Amurka sun yi mugunyar faduwa da sama da kashi 11 a rana daya, adadin da ba a taba gani ba shekaru da dama.

Faduwar dai ta kara yawan hasarar da aka samu ne a karshen makon da ya gabata.

Kuma matsalar ba wai a Amurka ta tsaya ba, ta shafi kasuwar hannayen jarin yankin Asia.

Fadar White House ta ce dama kasuwar hannayen jarin na iya canzawa lokaci zuwa lokaci.

Tun zabensa a watan Nuwamban 2016, Shugaba Donald Trump ke shelar samun ci gaba a kasuwar hannayen jarin a shafinsa na twitter, inda ya ke bayyana ribar da aka samu a darajar hannayen jarin.

Ba a taba ganin faduwar hannayen jarin ba a Amurka a tsawon shekaru shida.

Masana tattalin arziki sun ce masu hannayen jarin su shirya wa abin da kan iya faruwa da makomar kasuwar a watanni masu zuwa.

Wannan na iya zama wata damar sayen hannayen jarin, ko kuma matsala ce da za a ci gaba da gani.

Labarai masu alaka