Maryam Sanda 'na da cikin wata uku'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kalli yadda aka gurfanar da Maryam Sanda da 'yan uwanta

Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta, ta bukaci kotun Najeriya ta bayar da belinta domin ta je ta yi goyon cikin wata uku da take dauke da shi.

Lauyanta, Joseph Daudu (SAN) ya shaida wa kotun da ke Abuja, cewa ci gaba tsare Maryam a gidan yari ka iya yin illa ga jaririn da ke cikinta.

Ya kara da cewa bai taba ganin wani hukuncin kotu da ya amince a tsare macen da ke dauke da juna biyu ba sakamakon aikata laifi komai girmansa.

A watan Nuwamba ne dai aka gurfanar da Maryam a gaban kotun bisa zarginta da kashe mai gidanta, Bilyaminu Bello, bayan ta daba masa kwalba a kirji.

Sai dai a duk zaman kotun da ake yi Maryam ta sha yin watsi da tuhumar da ake yi mata.

Alkalin kotun mai shari'a Yusuf Halilu, ya ce zai yanke hukunci kan batun a ranar bakwai ga watan Fabrairu inda za su sake zuwa kotu domin ci gaba da shari'arta.

Wannan shari'a dai na ci gaba da jan hankalin jama'a a Najeriya ganin yadda mutane ke bibiyar lamarin a shafukan sada zumunta.

Image caption Maryam rike da jaririyarta a kotu

Labarai masu alaka