Tinubu ne zai jagoranci sasanta 'yan APC — Buhari

Bola Tinubu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bola Tinubu na cikin wadanda suka mara wa Buhari baya a zaben 2015

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin mutumin da zai jagoranci yunkurin da ake yi na dinke barakar da ke jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce tsohon gwamnan na Legas "zai shugabanci kokarin ganawa da sasanta da kuma inganta zaman da ake yi" a jam'iyyar.

Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu, ya ce ana sa ran Mr Tinubu ya shawo kan barakar da jam'iyyar ke fama da ita a sassan kasar da dama.

Jam'iyyar ta APC dai ta fada cikin rigingimun cikin gida tun bayan da ta lashe zaben shekarar 2015, lamarin da ya kai ga wasu 'ya'yanta ficewa daga jam'iyyar baki daya.

Rashin jituwar da ya fi kamari shi ne wanda ake yi tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da mutumin da ya gaje shi, Abdullahi Umar Ganduje.

Hakazalika ana fafatawa tsakanin gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da bangaren sanata Shehu Sani.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba a fayyace adadin lokacin da Bola Tinubu zai diba wurin sasanta 'ya'yan jam'iyyarba

Ana sa ran kwamitin da Bola Tinubu zai jagoranta zai yi sulhu a rikicin jam'iyyar APC da ke faruwa a Zamfara, Oyo, Kogi da dai sauransu.

Masu sharhi na ganin akwai gagarumin aiki a gaban Mr Tinubu, ganin irin rikice-rikicen da suka addabi jam'iyyar.

Wasu kuma na zargin cewa shi ma yana da sabani da wasu jigogin jam'iyyar a wasu sassan kasar.

Matakin da shugaban ya dauka ba zai rasa nasaba da karatowar zabukan shekara ta 2019 ba.

Labarai masu alaka