Elon Musk ya harba rokar dauke da mota zuwa duniyar Mars

Elon Musk's roadster Hakkin mallakar hoto Elon Musk/Instagram
Image caption Za a aika da wannan motar zuwa duniyar Mars - amma da wuya in zata kai ga doron duniyar

An yi nasarar harba wata roka zuwa sararin samaniya daga Florida da aka kera mafi karfi fiye da wadanda aka taba gani a baya.

Wani attajirin Amurka ne mai suna Elon Musk ya kera rokar da ya kira Falcon Heavy wanda aka bayyana cewa ta lunka abin da sauran rokokin da aka kera a baya ke iya dauka.

An harba rokar a cibiyar Kenedy ta zuwa sararin samaniya, a gaban idon Leroy Chiao tsohon kwamandan cibiyoyin zuwa sararin samaniya na duniya.

Mista Chiao ya shaidawa BBC cewa yanzu rokar ce mafi girma a duniya. "kuma kallon yadda ya tashi sama, ya nuna yana aiki lafiya lau ba wata tangarda" a cewar shi..

Yanzu Mista Musk zai yi amfani da wata tsohuwar motarsa ta tsere da zata iya kasancewa a kusa da rana a shekaru aru-aru.

Saboda yawan matsalolin da ake samu wajen harba sababbin roka a karon farko, an yanke shawarar aikawa da mutum-mutumi a maimakon dan Adam.

"Motar za ta kai kimanin kilomita miliyan 400 daga duniyarmu, kuma za ta rika tafiyar kilomita 11 a kowace dakika," kamar yadda ya gaya wa manema labarai ranar Litinin.

"Muna sa ran za ta rika zagaya duniyar Mars daga lokacin har zuwa daruruwan miliyoyin shekaru, kai watakila ma ta kai shekara biliyan daya."

Mista Musk ya kara da cewa za a sami hotuna masu "matukar birgewa" daga kyamara guda uku da aka makala wa rokan.

Hakkin mallakar hoto SPACEX
Image caption Za a harba rokan na Falcon Heavy daga cibiyar Kennedy Space Center

An harba rokar da misalin karfe 6:30 agogon GMT.

Kamfanin SpaceX, wanda mallakin Mista Musk ne ya yi kokarin harba rokan cikin sa'a uku a ranar Talata.

Hakkin mallakar hoto SPACEX
Image caption An gwada harba injinan rokan a karshen watan jiya
Hakkin mallakar hoto SPACEX
Image caption Rokan Falcon Heavy na da karfin wadannan rokokin uku gaba dayansu

Labarai masu alaka