'Yan sanda na neman mai magana da yawun Babangida

Kassim Afegbua Hakkin mallakar hoto Kassim Afegbua/Facebook
Image caption Kassim Afegbua

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta baza komar neman Kassim Afegbua, mai magana da yawun tsohon shugaban kasar Janar Ibrahim Babangida.

A wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan Jimoh Moshood ya fitar, ta ce Sifeto Janar na 'yan sanda ya bayar da umarnin a kama Mista Afegbua, sakamakon fitar da sanarwar bogi, da bata suna, al'amarin da zai iya jawo rigima a kasar.

A karshen makon da ya gabata ne Mista Afegbua ya fitar da sanarwar da ke cewa kada a zabi Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Sai dai daga bisani Janar Babangida ya karyata sanarwar inda ya ke musanta cewa rahotannin ba su yi daidai da kalaman da ya yi amfani da su ba a cikin sanarwarsa a kan batun.

Sanarwar rundunar 'yan sandan ta kuma: "Don haka ne rundunar 'yan sanda ke neman sa take kuma bukatar ya kai kansa ofishin 'yan sanda ma fi kusa a ko ina a kasar."

A ranar Lahadi ne Janar Babangida ya yi kira ga 'yan Najeriya da kada su zabi Shugaba Buhari a 2019.

A snaarwar da Mista Afegbua ya fitar a madadin tsohon shugaban kasar, ya nemi 'yan Najeriya da su zabi sabbin jerin shugabanni a zabuka masu zuwa.

Ya ce kamata ya yi shugaba Buhari ya fasa tsayawa takara a 2019 domin abin da kasar ke bukata kenan a yanzu.

Sai dai daga baya Janar Babangida ya fitar da wata sanarwar inda ya musanta abun da kakakin nasa ya fada da fari.

A ranar 23 ga watan Janairu, tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ma ya saki wata wasika inda yake kira ga shugaba Buharin da kada ya sake neman shugabancin kasar a 2019.

Labarai masu alaka

Karin bayani