Nigeria: NAFDAC ta kama manyan motoci biyu cike da Tramadol

woman wey dey troway fake drugs Hakkin mallakar hoto PIUS UTOMI EKPEI
Image caption NAFDAC tana kokarin magance matsalar shigo da kayan sa maye Nigeria

Hukumar da ke sa ido a kan abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta ce ta kama wasu manyan motoci biyu makare da maganin Tramadol.

Tramadol dai maganin rage radadin ciwo ne, amma yadda ake samar da shi da yawa ya sa mutane na amfani da shi ta hanyar da ba ta dace, kuma hakan ya kan sa su maye.

Darakta Janar ta NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye ce ta fadi hakan a Abuja ranar Litinin.

Ta ce bai kamata a dinga sayar wa da matasa Tramadol ba.

Farfesa Adeyeye ta ce, "Shan maganin ba bisa kaida ba yana yi wa kwakwalwa illa sosai, kuma ya kan sa mutum ya kasance cikin maye."

Ta kara da cewa: "A yanzu haka mun kama manyan motoci biyu makare da tramadol da safiyar Litinin. Ina za su? Za su je Ajegunle ne da Kano.

"Wa za su kai wa? Za su kai wa 'ya'yanmu ne! Don haka dole ne dukkanmu mu kawo dauki don yin wani abu. Wannan al'amari ne da ya shafe mu."

Farfesa Adeyeye ta ce matasa da dama sun mutu sakamon shan kwaya.

Shan kayan maye dai al'amari ne da ya zama ruwan dare gama duniya tsakanin matasa a Najeriya, inda al'marin ke zama abun tsoro da fargabar yadda al'mma za ta kasance nan gaba.

Labarai masu alaka

Karin bayani