An shiga yaki da al'adar tantance budurcin sabbin amare a India

Representational image of a bride and groom Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar wasu matasa a wani gari da ke jihar Maharashtra a yammacin Indiya ta shiga fafutukar kawo karshen wata al'ada ta tilasta wa sabbin amare tabbatar da budurcinsu a lokacin da suka tare a dakin miji.

Kamar yadda Marath Prajakta Dhulap ta rubuta

Anita mai shekara 22 ta ce irin takaicin da ta shiga a lokcin aurenta kan wannan al'ada, shekara biyu da ta wuce, har yanzu idan ta tuna ba abin da take yi sai kuka kawai.

Kamar sauran takwarorinta mata a garinsu na Kanjarbhat, mai mutane kusan 200,000 wadanda yawanc suke a jihar Maharashtra, an tilasta wa Anita yin wannan al'ada ta tantance budurci a ranar daurin aurenta domin a tabbatar da mutuncinta na ko ta riga ta san namiji a waje ko kuma ba ta sani ba.

Wannan al'ada ta zama wani daga cikin muhimman shika-shikan aure a cikin wannan al'umma, inda majalisar magabatan garin mai matukar iko ke tilasta wa amaren yin wannan gwaji.

Yadda ake wannan gwaji ko al'ada shi ne, za a ba wa ango da amaryar da za a yi wa auren farin zanin gado, sanna a je a kama musu daki a otal , wanda majalisar magabatan za ta biya ko kuma dangin amarya ko ango.

Ango da amaryar za su yi kwanciyarsu ta aure a wannan lokaci yayin da dangin amaryar da angon suke jira a waje. Idan amaryar ta jini a lokacin saduwar, to shi ke nan ta tabbata budurwa, amma idan ba ta yi jini ba to za a dauki tsattsauran mataki a kanta.

Ango yana da damar ya fasa auren, wato ya saki amaryar tasa idan a wannan kwanciya ta farko ba ta yi jini ba, sannan ita kuma amaryar sai a kunyata ta a bainar jama'a, har ma danginta su yi mata duka, saboda abin kunyar da ta jawo musu.

Wadannan mutane suna ci gaba da gudanar da wannan al'ada duk da bayanin da masana ke yi na karyata maganar cewa dole ne mace ta yi jini a saduwarta ta farko da namiji.

Akwai dalilai da dama da ba lalle ba ne mace ta yi jini a kwanciyarta ta farko da namiji, kamar yadda Dakta Sonia Naik, kwararriyar likitar mata da ke zaune a Delhi ta sheda wa BBC.

Likitar ta ce: ''Idan mace ta yi wasan motsa jiki sosai ko ta rika wasa da farjinta, domin jin dadi ta hanyar tura dan yatsa ko wani abu a ciki domin sha'awa, to bai zama lalle ta yi jini a lokacin saduwarta ta farko da namiji ba.

Haka kuma idan namijin da zai sadu da ita ya yi mata a hankali, musamman har su yi amfani da mai ko wani abu da zai saukaka shigarsa cikinta, to wannan ma na iya hana ta jini a saduwar ta farko.

To amma ita Anita a halin da ta samu kanta a ciki ta san cewa wannan gwaji na budurcin shirme ne kawai, domin ta riga ta sadu da mijin nata tun kafin su yi aure. Amma ta ce ita kam ba ta shirya ma abin da zai biyo baya ba na cin mutuncinta, idan aka gano cewa ai ta riga ta san namiji tun a waje.

Ta ce: ''Na dauka mijina zai kare ni a gaban wadannan 'yan majalisar magabata na garin namu, amma da suka tambaye shi, ina da tsarki ko ba ni da tsarki, wato ni cikakkiyar budurwa ce ko kuma a'a' sai ya nuna wannan zanin gado wanda ba alamar jini a jikinsa, kuma ya kira ni bogi.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana iya kashe aure idan amaryar ba ta da budurci, wato ba ta yi jini ba lokacin saduwar gwajin ta farko da mijinta

Ta kara da cewa: ''Abin ya ba ni mamaki, saboda ya rika tilasta min kwanciya da shi har tsawon wata shida. A nan take 'yan majalisar kauyen namu suka ayyana ni a matsayin maras tsarki, suka tafi suka ba ni wuri, aka bar ni ni kadai a nan ina ta kuka.''

An tilasta wa mijin Anita yin auren, wanda da farko ya so ya fasa saboda ta fadi wannan gwaji na budurci, bayan da wasu ma'aikatan kula da jin dadin jama'a sun ji abin da ya faru, suka kai maganar gaban 'yan sanda.

Sai dai ta ce mijin nata ya zamar mata wani dodo, kan yadda yake gana mata akuba, inda yake dukanta kullum da kuma muzanta ta.

Bugu da kari, abin takaicin shi ne majalisar magabatan garin ta haramta wa duk ma'auratan da amaryar ta fadi wannan jarrabawa ta budurci halartar duk wani taro ko biki na garin.

''Abu dai ba sassauci har lokacin da na samu juna biyu. Mijina ya takura min da tambaya : 'Dan wane ne wannan?' Su ma dattawan garin haka suke tambayarsa.'' In ji Anita.

Wata biyu da ya wuce mijinta ya kore ta da ita da jaririnta sabuwar haihuwa, saboda haka a yanzu tana zaune ne a gidan iyayenta. Amma ta ce kyamar da ta biyo bayan wannan gwaji na budurci da ta fadi ta shafi gidansu gaba daya, domin hatta kannenta sun rasa mazajen aure.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana bayyana amarya a matsayin cikakkiyar budurwa mai tsarki idan ta yi jini lokacin saduwar farko da mijinta (aka ga jinin ya bata farin zanin gado)