Yadda faduwar Dow Jones za ta shafi Nigeria

A halin da ake ciki yanzu dai kasuwar ta FTSE100 ta dan daidaita bayan da Dow Jones ta dan farfado da safiyar ranar Talata Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A halin da ake ciki yanzu dai kasuwar ta FTSE100 ta dan daidaita bayan da Dow Jones ta dan farfado da safiyar ranar Talata

Masu ruwa da tsaki a kasuwar hannayen jari ta Najeriya sun ce gabansu ba ya faduwa sakamakon faduwar da darajar kasuwannin Turai da Amurka.

A ranar Litinin ne dai kasuwar hannayen jari ta Dow Jones ta Amurka ta yi asarar kusan kashi daya cikin uku na darajarta, faduwa mafi muni tun shekarar 2011 - lamarin da ya jijjiga kasuwar FTSE100 da ke London da ma kasuwannin hannayen jari na Faransa da Jamus, da wasu kasashen nahiyar Asiya.

"Wannan lamari zai shafe mu ne kawai idan faduwar ta dore", in ji Malam Abubakar Aliyu, wani jami'i a kamfanin hadahadar hannayen jari na Tower Assets Management da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

A halin da ake ciki yanzu dai kasuwar ta FTSE100 ta dan daidaita bayan da Dow Jones ta dan farfado da safiyar ranar Talata.

A 'yan kwanakin nan dai darajar kasuwar hadahadar hannayen jarin ta Najeriya ta yi tashin da ba a ga irin sa ba a shekara tara - ko da yake ta fadi da kashi 0.87 cikin dari ranar Talata, wadda ita ce rana ta biyu a jere da darajar ta fadi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Litinin ne dai kasuwar hannayen jari ta Dow Jones ta Amurka ta yi asarar kusan kashi daya cikin uku na darajarta, faduwa mafi muni tun shekarar 2011

Wannan hauhawa da darajar kasuwar ta Najeriya ta yi dai ta faru ne sakamakon shigowar masu zuba daga waje.

Sai dai, a ganin Malam Abubakar, wadannan masu zuba jari na waje za su kwashe kudinsu daga kasuwar Najeriya ne kawai "idan farashin man fetur ya fadi."

Darajar kasuwar ta Dow Jones ta yi ta tashi a 'yan watannin da suka gabata (kamar yadda za a gani a hoton da ke kasa), har ma Shugaba Donald Trump kan yi tinkaho da hauhawar yana mai cewa salon mulkinsa ne ya haifar da ita.

Fargabar Babban Bankin Amurka ka iya kara kudin ruwa ce dai ta jawo masu zuba jari suke ta sayar da hannayen jarinsu suna sayen takardun lamuni, wadanda suka fi kawo riba idan kudin ruwa ya karu.

Wasu masana dai na ganin wannan ba wani abin tayar da hankali ba ne.

"Abin juyi-juyi ne. Wani lokaci darajar kasuwa za ta hauhawa, wani lokaci kuma ta yi kasa", in ji Malam Abubakar Aliyu.