Sana'ar kwalliya na biyan kudin sabulu

Makeup artist Hakkin mallakar hoto Getty Images

Bahijja Baba Shehu ta fara koyon sana'ar yi wa mata kwalliya ce saboda an kalubalance ta, amma sana'ar ta bude ma ta hanyoyin ci gaba.

Amma sana'ar kwalliya ta zo wa Bahijja ne sanadiyyar wata zolaya da aka yi mata.

"Tun lokacin da za a yi bikin wata yarmu ne a lokacin muna jami'a, sai wata mata ta zo daga Jos".

Ta kara da cewa, "Sai na ce idan nawa bikin ya zo, ni zan wa kaina kwalliya. Sai aka yi min dariya. To dariyar da aka yi min ce ta sa na dage har na fara koyon yadda ake yin kwalliyar."

Amma Bahijja wadda ta fara wannan sana'ar ne tun shekara ta 2012, ta ce sun fi yi wa amare da wadanda suka haihu wannan kwalliyar, da kuma masu bikin zagayowar ranar haihuwarsu.

Bahijja Baba Shehu ta tattauna da wakiliyar BBC, Halima Umar Saleh a shagonta da ke birnin Kano, kuma ga yadda hirar ta su ta kasance.

A ina kika koyi sana'ar kwalliya?

"A Malaysia. A lokacin a can nake karatun Jami'a. Idan aka tashi daga makaranta, sai in tafi in koya, haka ma nake yi idan ana hutu. Kuma biyan kudi nayi na koya".

Nasarorin da ta samu a sana'ar:

"To na dai fara sana'ar ne a Zoo Road, Kano, a lokacin ina da wani shagon sayar da kaya. Daga baya abin ya bunkasa har muka bude cibiyar koyar da kwalliya. Na kuma bude Salon da ya kunshi masu taya ni aikin yin kwalliyar da dama. A tsohon wurin namu na Zoo Road na fara bude makaranta, inda mutane ke biya domin a koya musu sana'ar ta kwalliya, wato make-up".

Daga wadanne sassa daliban wannan makarantar ta ki suka fito?

Kuma yawancin dalibanmu daga wajen Najeriya suka fi zuwa. Kamar daga Nijar, Ghana, Kamaru, da Kwatano. Ga wata 'yar Laberiya ma da ko Hausa bata ji".

Nawa ne daliban da ke makarantar, kuma ma'aikatanki nawa ne?

"Dalibai na za su kai 10, ma'aikata kuma bakwai nake da su".

Nawa ki ke karba, a misali, idan za ki yi wa amarya kwalliya?

"Daga Naira 30,000 har zuwa 50,000. Ya danganta ga yadda cinikin ya kaya."

Wadanda ba amare ne ba fa?

"Muna karabar Dubu 6 zuwa dubu 6,500".

Kalubalen da ta fuskanta

To wadannan matsaloli ki ka fuskanta?

"Harka da jama'a abu ne mai wuya, kuma akwai batun kula da wuri, su wuta ruwa da haraji. Akwai kuma kudin haya da sauran hidimomi. Amma mu na so a sassauta mana a wajen kudaden da gwamnati ke karba na haraji".

Har kwana nawa kwalliyar ke kai wa kafin a sake yinwata?

"Wasu amaren na yin kwalliyar misali a yau, sai kuma su barta har ta kwana, amma ina iya cewa kyau dai a yi ta daga safe zuwa dare".

Yaya ake share kwalliyar bayan an gama biki?

"Ba da ruwa ake goge kwalliyar ba. Ana amfani da wasu kananan tawul-tawul ne masu kama da baby wipes wajen goge ta".

Daga ina kike sayen kayan kwalliyan da ki ke amfani da su?

"Wasu a Legas nake sayensu, wasu kuma ina odarsu ne daga Amirka".

Ta yaya ki ke iya hada aikin gida da sana'arki, ganin cewa ke matar aure ce?

"Shi yasa yake da kyau ki sami sana'arki ta kanki. Wannan sana'ar ba da wuri ake fitowa ba. Da misalin karfe biyu na rana muke fara wa. Kin ga na riga na kammala aikin gida, sai in fito wajen sana'a zuwa yamma".

Tasirin shafukan sada Zumunta:

Gaya mana yadda shafukan sada zumunta kamar Instagram da Facebook suka yi tasiri a wannan sana'ar taki.

"Shafukan sada zumunta sun yi tasiri sosai wajen tallata sana'armu. Domin wadanda suke zuwa daga wajen Najeriya ma ta kafafen sada zumunta suke samun bayanai game da mu. Kuma mun fi amfani da shafin Instagram. Mu kan saka wasu hotuna a Facebook amma Instagram muka fi amfani da shi."

To a karshe mene ne burinki?

"Ina da burin fadada wannan sana'ar, da karo ma'aikata nan gaba".

Labarai masu alaka