'Jacob Zuma zai ba da kai...'

Zuma
Bayanan hoto,

Jacob Zuma ya amince zai sauka da sharadin amincewa da wasu bukatunsa.

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma da ya yi ta kokarin baudewa a baya, a yanzu haka rahotanni sun ce yana shirin amincewa da kiraye-kirayen ya yi murabus daga kan kujerar mulkin kasar.

Mista Zuma da ke fuskantar zargin rashawa ya gana da shugaban jam'iyyarsa ta ANC Cyril Ramaphosa, kuma bayanai sun ce ya amince zai sauka da sharadin amincewa da wasu bukatunsa.

Wakilin BBC ya ce hakan ya nuna ANC na dab da shawo kan Zuma, amma ya ce sun samu labarin cewa akwai wasu bukatu da Zuma ke son a amince kafin ya sauka.

Ya ce yana da wahala a amince a ba shi kariya, amma shugaban na neman a ba shi goyon baya domin kare kansa a kotu.

Tuni dai aka dage babban jawabin halin da kasa take ciki da ya kamata Shugaba Zuma ya gabatar a ranar alhamis.

Jiga-jigan jam'iyar ANC dai sun ta kai ruwa-rana domin ganin shugaban ya mika mulki ga Ramaphosa, inda ya yi watsi da bukatar bayan sun tunkare shi a gidansa da ke Pretoria.

Shugabannin ANC na kokarin ganin sun dinke barakar da ta kunu kai a cikin jam'iyar domin kawar da rabuwar kai tare da kare martabarta kafin zabe mai zuwa.