An yanke hukuncin kisa kan wanda ya kashe wanda 'ya yi ridda'

Pakistani protesters with banners demanding justice for Mashal Khan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kisan dalibin ya jawo suka

Wata kotu a Pakistan ta yanke hukuncin kisa kan wani mutum da kuma daurin rai-da-rai ga wasu mutum biyar din, sakamakon kisan wani dalibi da suka yi, wanda suke zargin sa da yin ridda.

An kuma samu wasu mutum 25 din da kananan laifuka a cikin lamarin, sannan kuma aka wanke mutum 26 da cewa ba su da laifin komai.

Gungun mutanen ya kashe Mr Khan ne bayan an fito da shi da karfin tuwo daga cikin Jami'arsa da ke arewa maso yammacin kasar a watan Afrilun 2017 saboda zarginsa da yin ridda.

Sun lakada masa duka kafin su harbe shi sannan suka daddatsa jikinsa.

An rika gudanar da shari'ar ne a cikin babban kurkukun Haripur saboda dalilai na tsaro.

An tsaurara matakan tsaro a kusa da gidan yarin gabanin yanke hukuncin, sannan aka kai daruruwan 'yan sanda, aka kuma rufe hanyar da ke zuwa gidan yarin.

An kama mutum 57 da hannu a zargin kisan da aka yi wa Mr Khan, cikinsu har da shugabanninsu uku.

Image caption An girke jami'an tsaro
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Dakin Mashal Khan da ke Jami'ar Abdul Wali Khan
Image caption Mahaifin Mashal Khan ya bukaci gwamnati ta dauki mataki

Labarai masu alaka