Ana binciken likitan-bogi da ya yi wa mutane allurar HIV a India

Mutanen da ke fama da HIV a India sun ragu da kshi 50 cikin 100 cikin shekara goma Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutanen da ke fama da HIV a India sun ragu da kshi 50 cikin 100 cikin shekara goma

Jami'ai a India na gudanar da bincike kan ikirarin da aka yi cewa wani likitan bogi ya yi wa akalla mutum 33 allura da sirnji mai dauke da cutar HIV.

Ana zargin likitan bogin da yin amfani da sirinji da ya yi wa masu dauke da HIV allura wurin yi wa mutanen da ke fama da mura da tari a jihar Uttar Pradesh.

Jami'an kiwon lafiya na tarayyar kasar za su kai ziyara lardin Unnao, inda lamarin ya faru, domin gudanar da bincike kan batun.

An yi zargin cewa mutumin ya karbi kudin kasa, wato rupee goma kan kowacce allura da ya yi.

Ba a tabbatar da adadin mutanen da ya yi wa allra da sirinjin ba.

Wani likita da ke cikin masu binciken Dr Tanymay Kakkad ya shaida wa jaridarThe Indian Express cewa "Binciken likitoci ya nuna cewa kasadar kamuwa da cutar HIV tana kai 0.3% idan aka yi wa mutum allura da sirinjin da ke dauke da cutar saboda kwayar cutar ba ta jurewa yaduwa cikin iska."

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato jami'ai na cewa mutum 33 da aka tabbatar sun kamu da HIV na cikin mutum 566 da aka yi wa gwajin cutar a wani gangami da gwamnati ta hada.

Labarai masu alaka