Shin Bola Tinubu zai iya sasanta rikicin APC?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ra'ayoyi: Ko Tinubu zai iya sasanta rikicin APC?

Nadin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa fitaccen dan siyasa Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a matsayin mutumin da zai jagoranci yunkurin da ake yi na dinke barakar da ke jam'iyyar APC mai mulkin kasar, ya sa masana harkoki siyasa sun soma nazari kan yadda za ta kaya.

Wata sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce tsohon gwamnan na Legas "zai shugabanci kokarin ganawa da sasanta da kuma inganta zaman da ake yi" a jam'iyyar.

Wannan dai babban aiki ne da ba a taba yin irinsa ba tun bayan da aka kafa jam'iyyar a shekarar 2013 gabanin zaben 2015, in ji Malamin da ke koyar da sha'anin siyasa a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta Kano, Mallam Kabiru Sa'idu Sufi.

APC ta hau karagar mulki ne bayan da Shugaba Buhari ya kayar da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan - karon farko da jam'iyyar adawa ta taba kafa gwamnati a tarihin Najeriya.

Mallam Sufi ya shaida min cewa "Rikicin da jam'iyyar APC ta fada ba karami ba ne, musamman idan aka yi la'akari da cewa bangarori daban-daban ne da ke da bukatu daban-daban suka kafa ta, amma aka watsar da wasu tun bayan da aka ci zabe."

A kwanakin baya wani mai sharhi a kan sha'anin siyasa kuma Malami a Jami'ar Abuja, Dr Abubakar Kari, ya shaida wa BBC cewa rikicin APC ya samo asali ne sakamakon rashin tsoma bakin Shugaba Buhari cikin harkokin jam'iyyar bayan da aka yi nasara a zaben 2015.

"Babbar matsalar jam'iyyar APC ita ce har yanzu ba ta zama dunkulalliyar jam'iyya ba; har yanzu gungu-gungu na 'yan jam'iyyu daban-daban ne irinsu tsohuwar jam'iyyar ACN da CPC da kuma tsohuwar PDP.

Babu wanda yake kallon APC a matsayin jam'iyya, kuma hakan ne ya sa ake fuskantar manyan matsaloli a jam'iyyar," in ji shi.

Image caption Jihohin da ke fama da rikici a jam'it=yyar APC

Wani babban batu da ya nuna cewa zama ake irin na gidan haya a APC shi ne yadda tun da aka zo zaɓen shugabannin majalisar dokokin tarayya 'yan jam'iyyar ta APC suka ƙi zaɓar mutanen da jam'iyyar ta tsayar, abin da Dr Kari ya ce ya dasa dambar rashin jituwa tsakanin manyan 'yan jam'iyyar.

Kazakila rigingimun cikin gida da suka barke a rassan jam'iyyar na jihohi da kuma yadda suka yi kamari ba tare da an shawo kansu ba sun yi wa APC illa sosai, in ji Mallam Kabiru Sufi.

"Ka duba rashin jituwar da ta yi kamari tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da mutumin da ya gaje shi, Abdullahi Umar Ganduje da kuma matsalar da ta sa aka ja layi tsakanin Gwamna Nasir El-Rufai da bangaensu Sanata Shehu a jihar Kaduna da kuma matsalar da ta sa su Sadiq 'Yar Adua suka kafa APC Akida a Katsina.

"Haka kuma idan ka duba za ka ga akwai rikici tsakanin 'yan jam'iyyar a jihohin Zamfara da Gombe da Kogi da ma wasu jihohin da ke kudancin kasar.

Wannnan na faruwa ne baya ga rashin katabus din jam'iyyar a matakin tarayya. Duk da haka babu wani cikakken mataki da Shugaba Buhari ya dauka na tsawatarwa wadannan bangarori sai yanzu."

Jihohin da jam'iyyar APC ke fama da rikici

 • Kano: Tsagin Kwankwasiyya da Gandujiyya
 • Kaduna: Bangaren Gwamna Nasiru El-Rufa'i da Sanata Shehu Sani
 • Gombe: Bangaren Sanata Danjuma Goje da Sanata Usman Nafada
 • Kogi: Bangaren Gwamna Bello da Sanata Dino Melaye
 • Bauchi: Bangaren Gwamna M.A Abubakar da Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara
 • Borno: Bangaren Sanata Abu Kyari da Gwamna Kashim Shettima
 • Niger: Gwamna Sani Bello da wasu 'yan majalisar tarayya
 • Jigawa: Gwamna Badaru Abubakar da bangaren Ubale Hashim
 • Ogun
 • Ondo
 • Plateau
 • Cross River

'Tinubu na da jan aiki'

Irin wadannan rikice-rikicen da suka addabi jam'iyyar sun sa ana ganin akwai kalubale a gaban Mista Tinubu.

Mallam Sufi ya ce fitaccen dan siyasar zai iya yin galaba a aikin nasa idan aka yi la'akari da irin rawar da ya taka wajen ganin an kafa jam'iyyar APC har ta yi nasara a zaben 2015.

"Ina da yakinin cewa zai iya shawo kan matsalolin da ke APC saboda akasarin mutanen da ke rikicin suna ganinsa da mutunci matuka. Kuma dama an ci gaba da rikicin ne saboda babu wanda ya sanya baki.

An dade ana zargin cewa babu akida a tsarin siyasar Najeriya, kuma 'yan siyasar kasar bukatarsu ce a gabansu, don haka idan kowannensu ya samu wani bangare na abin da yake bukata a jam'iyyar, to za a sasanta.

Wasu kuma na hasashen cewa ba lallai ba ne wadanda aka bata wa su so ficewa daga jam'iyyar ba ganin cewa har yanzu babu wata jam'iyyar da ke da karfi irin nata.

Daya daga cikin mutanen da ke rigima a jihohinsu, Sanata Shehu Sani, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa kwamitin da Asiwaju Tinubu zai jagoranta "shi ne dama ta karshe ta samun zaman lafiya a jam'iyyar APC."

Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY

Tasirin kungiyar Obasanjo

A cewar masanin, har yanzu PDP ta kasa zama jam'iyyar adawa ta hakika, sannan babu wasu daidaikun jam'iyyu masu karfi sosai da za su iya kalubalantar APC.

A daidai lokacin da zaben 2019 ke kara karatowa, wasu na ganin duka APC da PDP ba mafita ba ne ga matsalolin da kasar ke fuskanta, a don haka a kwai bukatar samar da wani zabin na daban.

Daya daga cikin masu irin wannan tunani shi ne tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, wanda ya kafa wata kungiya da nufin kawar da dukka manyan jam'iyyun biyu.

Amma Mallam Sufi na ganin "da wuya ta yi tasiri" saboda irin kallon da ake yi masa na "mai-baki biyu".

Sai dai wasu na zargin cewa shi kansa Asiwaju Tinubu yana da sabani da wasu jigogin jam'iyyar a wasu sassan kasar, ciki har da yankinsa na kudu maso yamma.

Hakkin mallakar hoto KANO STATE GOVERNMENT
Image caption Rikicin da ake yi tsakanin Kwankwaso da Ganduje ka iya shafar Shugaba Buhari

Mai sharhi kan sha'anin siyasar ya ce duk da irin wannan matsaloli, hamshakin dan siyasar zai iya dinke barakar da ke APC.

A cewarsa, "Su mutanen kudu maso yamma ci gaban kasa ne a gabansu don haka komai rigimar da suke yi idan suka ga abin da zai amfane su za su ajiye rigimar su rungume shi".

Ya kara da cewa akwai yiwuwar manyan shugabannin jam'iyyar da ke matakin tarayya za su so ganin an yi sulhu a jam'iyyar domin idan aka yi hakan su za su ci riba.

Masu sharhi na ganin Shugaba Buhari ya dauki matakin hada kan 'yan APC ne saboda kokarinsa na sake yin takara a zaben 2019, ko da yake har yanzu bai bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar ba.

'Yan kasar da ma 'yan siyasa za su so ganin yadda Asiwaju Tinubu zai tunkari wannan babban aiki da ke gabansa, kuma masana na ganin dinke barakar jam'iyyar APC ko akasin hakan zai yi tasiri sosai a zabukan shekarar 2019.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Labarai masu alaka