Nigeria: Zaki ya kashe mai kula da shi a Kaduna

Mamacin a gadon asibiti gabannin ya rasu Hakkin mallakar hoto Nura Ringim
Image caption Mamacin a gadon asibiti gabannin ya rasu

Mai kula da namun dajin da wani zaki ya kai wa farmaki a Kaduna da ke arewacin Najeriya ya rasu.

Mutumin mai suna Mustafa Adamu, ya rasu ne sanadiyyar raunukan da ya samu yayin da zakin ya yayyaga shi bayan ya kufce daga kejin gidan zoo da aka killace shi.

Al'amarin ya faru ne a ranar Asabar a filin shakatawa na Gamji Gate, inda mutane da dama suka tsallake rijiya da baya sakamakon kufcewar zakin.

A wani jawabi da mamacin ya yi wa maneman labarai kafin ya rasu, ya ce zakin ya samu kufcewa ne bayan ya kammala ba shi abinci.

"Da misalin 12 na rana abun ya faru, na yi kuskuren barin wani waje da ya kamata a ce na rufe a bude ne, sai kawai ya sulalo ya fito ta wajen.

"Da fitowarsa sai ya yo kaina ya turmushe ni, sai abokan aikina suka ankara suka yi wa zakin tsawa, sai ya arce.

"Sai na ji abokan aikin nawa sun fara salati, nima sai na fara amsa wa. Daga bisani suka dauke ni daga wajen aka yi asibiti da ni."

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Saurari yadda matar Mustafa ta rabu da shi kafin ya gamu da ajalinsa

Akasarin raunukan da mamacin ya samu dai a wuya ne, wurin da dama namun daji kamar zaki kan hara in sun kai farmaki.Mustafa dai ya shafe tsawon wata takwas yana kula da zakin da ke Gamji Gate.Rahotanni dai na cewa an sami sauyi ne na masu kula da baki dayan wurin shakatawar har ma da wurin ajiye namun dajin, inda aka sallami wadanda aka bai wa horo na tunkarar namun daji aka kuma kawo wasu dabam.

Tuni dai aka yi jana'izar mamacin.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da zaki ke kashe mai kula da shi ba a Najeriya. Ko a watan Satumbar 2017 ma wani zaki ya kashe mai kula da shi a gidan ajiye namun daji da ke birnin Oyo na jihar Ibadan.

A watan Disambar 2015 ma wani zaki ya kufce daga gidan namun daji na Jos a jihar Plateau, amma bai kashe kowa ba, sai dai daga bisani an harbe zakin.

Labarai masu alaka