Hotunan zanga-zangar karin farashin fetur a Ghana

A ranar Laraba ne al'ummar kasar Ghana da dama suka fito yin zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur.

Bayanan hoto,

A ranar Laraba ne al'ummar kasar Ghana da dama suka fito yin zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur.

Bayanan hoto,

Suna so gwamnati ta dauki matakan da za su rage radadin da hakan zai jawo a kan al'umma a kasar.

Bayanan hoto,

MAsu zanga-zangar sun sanya jajayen kaya da bakake, su ka yi ta bi kan manyan titunan birnin Accra, suna ihun "Shugaban kasa ka rage farashin man fetur, ba wannan alkawarin kayi mana ba."

Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar na kukan cewa farshin man fetur na ta hauhawa, al'amarin da ke sanya rayuwar mutane a wahala.

Bayanan hoto,

Sun yi korafin cewa fetur ya yi tsada inda lita daya ta zarce dala daya, kuma albashi ba ya isar mutane harkokin rayuwa.

Bayanan hoto,

Kamfanin man fetur na kasar ya ce ba shi ke sanya farashin mai ba, kuma yana bakin kokarinsa don rage radadin da mutane ke ciki.

Bayanan hoto,

Duncan Amoah jagoran wannan zanga zanga sanye da bakar riga da Jan kyalle akan sa

Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar sun bai wa gwamnati mako biyu ta sauya wannan mataki.