Yadda harin 'makami mai guba' ya rutsa da jarirai a Syria

Ku latsa alamar hoton da ke sama don kallon bidiyon, amma yana iya daga muku hankali.

Dakarun gwamnatin Syria da na Rasha na zafafa kai hare-haren sama a yankin da ke karkashin ikon 'yan tawaye tun bayan da aka harbo wani jirgin yakin Rasha a karshen makon da ya gabata.

An kuma samun rahotannin harin gubar gas. Gwamnatin Syria dai ta sha yin watsi da zargin da ake mata cewa tana kai hari da makamai masu guba.

Harin da aka kai a baya-bayan nan shi ne na Idlib, yankin da har yanzu ke karkashin ikon 'yan tawaye, amma tun bayan shiga sabuwar shekarar nan an samu rahotannin wasu hare-haren da aka kai wajen birnin Damascus da ke gabashin Ghouta.