An gano wani zanen dan Nigeria a Landan

Hakkin mallakar hoto Bonhams
Image caption Zanen ya kasance wata alama ta sasantawa bayan yakin basasar da aka yi a Nigeria

An gano wani zanen da mai matukar daraja da wani dan Najeriya ya yi a wani gida a London.

Zanen da Ben Enwonwo ya yi tun shekarar 1974, na wata gimbiyar yarabawa ta masarautar Ile Ife, wadda ake cewa Adetutu Adeiluyi, wadda aka fi sani da Tutu, ya bace tun sama da shekaru arba'in da suka wuce.

Zanen ya kasance wata alama na sulhun da aka yi bayan yakin basasar kasar da aka yi tsakanin gwamnatin Nigeria da yankin Biafra.

Ana kyautata zaton cewa darajar zanen kan iya kai fam dubu 300 idan an sayar da shi a kasuwar gwanjon kayayaki, wanda tarihi ne da wani dan Nigeria mai zane zane ya kafa a zamanin da mu ke ciki.

Ben Okri wanda marubucin litafi ne da ya taba kashe gasar rubuta litafi ta Booker ya bayanna zanen a matsayin wani muhimin abu da aka gano a fasahar zane zanen Afrika a cikin shekaru 50 da suka gabata.

Ya kuma ce wannan abun farinciki ne .

Mr Enwonwu ya yi zane zane guda uku na gimbiya Tutu, sai dai dukaninsu sun bata a shekaraR 1994 bayan mutuwarsa.

Kawo yanzu ba a san makomarsu ba.