Ba daidai ba ne kayyade yawan jam'iyyu — Jega

Babu batun kayyade jam'iyyun siyasa a Najeriya inji Jega Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Babu batun kayyade jam'iyyun siyasa a Najeriya inji Jega

Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya ce bai kamata ace an kayyade yawan jam'iyyun siyasa ba a Najeriya, saboda dimokradiyya a ko ina a kan bari duk wanda yaga zai iya kafa jam'iyya, to ya fito ya kafa, sannan kuma ya yi kokarin jan ra'ayi jama'a wadan da za su mara masa baya har su samu nasara idan lokaci zabe ya yi.

Farfesa Jega, ya shaida wa BBC, haka ne a matsayin ra'ayinsa kan shawarar da tsohon shugaban Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayar a kan takaita yawan jam`iyyun siyasa zuwa biyu kwarara a kasar.

Tsohon shugaban hukumar ta INEC, ya ce duk wasu kasashe da suka ci gaba, ba kasar da aka fara da cewa an tantance sai jam'iyyu biyu.

Farfesan ya ce " Idan jam'iyyu da yawa suka fito to a haka za ayi ta tantancewa har wasu suyi karfi".

Obama da Jega ne suka kayar da ni a zaben 2015 - Jonathan

Kun san ranakun da za a yi zaben 2019 a Nigeria?

Ya ce, a dimokradiyya komai na fadakarwa da fahimta da kuma ra'ayi ne.

Don haka ba zai yi wu ace an ja layi mutane jam'iyyu biyu kawai za su bi ba.

Farfesa Jega, ya ce a ba wa mutane zabi, da sannu a hankali sai su fahimci waccece jam'iyyar gaskiya har su karkata kai.

To sai dai kuma farfesan ya ce, akwai ka'idoji da sharudda da a kan zayyana ga jam'iyyun da suke fitowa domin takara, kuma dole sai sun cika wadannan sharudan kafin su tsayar da dan takara.

Farfesa Jega, ya ce " Ina ganin dan lokacin da ya rage a yi zabe a Najeriya, gaskiya ba zai bada wata dama ga wata jam'iyya ta fito ta ce zata samu kafuwa ba, sai dai idan wasu jam'iyyun ne za su hadu, shi ma ina kokanto a kan cewa ba lokacin da za a iya hakan".

Labarai masu alaka