Dana Air ya zargi fasinja da jawo faduwar kyauren jirgi yayin sauka

Dana Hakkin mallakar hoto Ola Brown Twitter

Wani kamfanin jiragen sama a Najeriya ya dorawa wani fasinja laifin zama sanadin faduwar da kyauren wani jirginsa ya yi yayin da ya zo sauka.

Kamfanin jirage na Dana ya ce abu ne mai matukar wahala a ce kyauren jirgin sama ya fadi da kansa "in dai ba wani fasinja ne ya yi kokarin bude shi ba.'

Tun a ranar Laraba da abun ya faru masu amfani da shafin sada zumunta na Twitter suka fara yada batun cewa rashin kula da al'amura ne daga kamfanin ya sa hakan faruwa.

Jirgin ya tashi ne daga Lagos don zuwa abuja babban birnin kasar inda a wajen sauka sai kyauren jirgin ya bude ya fadi.

Amma dai wani mai magana da yawun kamfanin Dana ya ce, "Babu yadda za a yi a ce kyauren na rawa saboda babu wata iska da ke shiga cikin jirgin.'

Kamfanin ya kuma kara da cewa kafin jirgin ya tashi sai da injiniyoyi da kuma tawagar jami'an Hukumar Kula da Zirga-zirgar jiragen sama suka duba jirgin tsaf, "ba su kuma samu wani abu da ke nuna akwi matsala ba."

Mai magana da yawun kamfanin ya kuma kara da cewa: "Jirgin ya yi lattin tashi da minti takwas ne kawai saboda mun tsaya nunawa fasinjoji yadda za su kula da kansu saboda tsaro da kariya yayin da jirgi ke lulawa."

Labarai masu alaka