North Korea ta yi faretin soji gabanin gasar Olympics

North Korean military vehicles pass through Kim Il-Sung square during a mass military parade in Pyongyang on October 10, 2015. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sojin Koriya ta Arewa na fareti a birnin Pyongyang

An yi faretin sojoji a Koriya Ta Arewa wanda shugaban kasar Kim Jong-un ya halarta, kwana daya kafin a bude gasar Olympics ta hunturu a makwabciyar kasar wato koriya Ta Kudu.

Koriya ta Arewa ta rika bayyana ranar yin faretin da ta yi a shekarun baya, amma a bana an nuna faretin a talabijin ne bayan da aka kammala shi.

An saba gudanar da faretin a watan Afrilu na ko wacce shekara, kuma masu nazari na ganin yin sa a wannan lokacin ya kasance wani koma baya ga yunkurin sasantawa da kasashen biyu na Koriya suka fara yi a wannan lokacin na Olympics.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
An yi ta wa Kim Jong-un da matarsa Ri Sol-ju kirari a wajen faretin

Amma Koriya ta Kudu ta sanar da cewa shugabanta zai sadu da tawagar 'yan wasa daga Koriya ta Arewa ranar Asabar.

Moon Jae-in zai halarci liyafar cin abinci da 'yan wasa 22 na Koriya ta Arewa.

A cikin jami'an da za su halarci liyafar daga Arewa akwai shugaban kasar mara cikakken iko, Kim Yong-nam da Kim Yo-jong, wadda 'yar uwar shugaba Kim Jong-un ce.

Ana sa ran ita ce mambar majalisar zartaswar Koriya ta Arewa ta farko da za ta ziyarci Koriya ta Kudu.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An yi faretin na bana don bikin shekara 70 da kafa rundunar sojin Koriya ta Arewa

Faretin na bana bai kai girman na shekarun baya ba. An nuna shugaba Kim Jong-un na duba faretin sojin kasar tare da matarsa Ri Sol-ju.

An yi faretin na bana don bikin shekara 70 da kafa rundunar sojin Koriya ta Arewa, amma wannan ne karo na farko da aka gudanar da shi a watan Fabrairu.

Ya ya halin siyasa ya ke tsakanin kasashen biyu?

Kasashen biyu za su gudanar da wasanni a karkashin tuta daya a gasar ta Olympics da za a yi bikin budewa ranar Juma'a.

Shugaban Koriya ta Kudu, Moon Jae-in zai gana da tawagar 'yan wasa na Koriya ta Arewa, amma ba a fadi wurin da za su hadu ba.

Hakkin mallakar hoto KCNA
Image caption Kim Yo-jong tare da dan uwanta shugaba Kim Jong-un a lokacin da suke rangadin wani barikin sojin kasar a 2015

Wakilan Koriya ta Arewan za su isa Koriya ta Kudu ranar Jumma'a ta jirgin sama.

Amma Koriya ta Arewa ta ce ba ta da niyyar haduwa da jami'an Amurka a wurin bikin na Olympics.

Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence zai isa Koriya ta Kudu ranar Alhamis kuma zai gana da Mista Moon.

An kuma tabbatar da cewa 'yar uwar shugaba Kim Jong-un za ta ziyarci bikin bude Olympics din a ranar Juma'a.

Labarai masu alaka