Wata mata ta zargi mijinta da sace mata koda maimakon sadakinsa

Blue-gloved hands of medical latex exchange a surgical scissors, while a third hand can be seen holding a clamp and cotton swab Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matar ta yi zargin cewa an cire mata koda ba tare da saninta ba

'Yan sanda a Indiya sun kama mijin wata mata da kanin mijin bayan da ta ce sun sace mata koda guda daya a maimakon sadakin da mijin ke bin ta.

Kafofin yada labaran kasar sun ce mijin matar wanda dar yankin yammacin Bengali ne, ya shirya cewa a yi mata tiyata don cire ciwon appendicitis, sakamakon fama da take da ciwon ciki tsawon wata biyu.

A karshen shekarar 2017 ne, bayan da aka yi mata binciken lafiya sau biyu aka gano cewa koda daya ce ta saura a cikinta.

Ta yi zargin cewa mijinta ya sha neman ta biya shi sadaki.

Tun shekarar 1961 ne aka haramtawa mata bai wa maza sadaki a Indiya, wanda haka abun yake a al'adance.

Da take magana da kafofin watsa labarai, matar mai suna Rita Sarkar, ta ce an shafe shekaru mijinta na gallaza mata da cin zarafinta saboda ba ta ba shi sadaki ba.

Jaridar Hundustani Times ta ruwaito matar na cewa, "Mijina ya kai ni wani asibiti mai zaman kanta a Kolkata, inda ma'aikatan wajen suka ce min zan ji sauki bayan an cire cutar appendicitis din ta hanyar yin tiyata."

"Mijina ya gargadeni cewa kar na gaya wa kowa cewa an yi min tiyata a Kolkata."

Watanni bayan nan, sai ta fara rashin lafiya, inda wasu 'yan uwanta suka kai ta wajen wani likita.

Hoton ciki da aka dauka ya nuna cewa ba ta da koda daya ta hannun dama. Da aka sake yi mata binciken lafiya sai aka sake tabbatar da hakan.

"Daga nan ne na fahimci dalilin da ya sa mijina ya ce kar na gayawa kowa maganar tiyatar da aka yi min a Kolkata,' in ji Rita Sarkar.

"Ya sayar da kodata saboda iyayena sun kasa biyansa sadaki."

Labarai masu alaka